Ziyarar wakilan Shafin Jaridar Ma'asumah ga Shahid Ishaq Muhammad Suleman.

 



Ma'asumah Nigeria News update

Maziyarta suka kasa hakuri su tafi saboda Shakuwa da Soyyaya Haka suka kama Ziyara Shahidin ɗaya bayan ɗaya A lokaci ɗaya, ba abunda kakeji a wajen sai sautin kukan bayin Allah badan ya yi Shahada sukewa kika ba a'a, saboda Mahimmancin sa a cikin su da Halayen shi. Na gargaru da iya zaman takewar shi da mutane, duk cikin Wakilan “ SHAFIN MA'ASUMAH ” suna son kancewa tare da Shahid Ishaq Muh'd Suleman Amma yau gashi an wayi gari ba a tare da shi sai dai Ziyara wannan kewar ce ta sa bayin Allah Kuka a wajen.

Bayan Haka Dan uwa Ammar Usman Sabo ya yi wasu bayanai a wajen lokacin da ake Ziyara na so a ce na riƙe jawabin saboda Mahimmancin su ya da ce a ce na kawo, kowa ya ji Amma a yi afuwa. Saboda Gazawata ta sa na kasa riƙewa amma a cikin Bayanan nasan Zan iya tuna inda yake cewa yanzu shi shahid 'Ishaq' ya Huta. Ya gama aikin sa mune kawai ya rage muyi namu aikin, yake cewa Shahid na da Hakƙi akanmu idan muka kasa saukewa wallahi zai ƙalubalance mu, dan haka ya rage na mu yin abunda ya ta ce ga Shuhada dansu sunyi da ce sun wuce wajen tasu ta yi kyau.

Allah sarki zan iya tuna loƙacin da zamu wuce mubar makwancin nike cewa Auwal M Tukur; na ce Allah sarki a Kano na fara ganin Shahid. Gani na farko gashi gani na biyu ya zama Ziyarar Makwancinsa ne ya Allah Amincin Allah ya tabbata ga ( Shahid Ishaq Muhammad Suleman ); tun Ranar da aka Haifesa da ranar da kayi Shahadar sa har izuwa Ranar, da za a tasheka kana Mazlumi.

27/12/2022

3-1444

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post