@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@
Tabbas duk Wanda Yasan Tarihin Ɗariƙar ƙadiriyya a Duniya Yasan Cewa Ɗariƙar Ƙadiriyya itace mafi Ƙololuwar Ɗaɗewa a duk Ɗariƙun Duniya....
Tabbas Mallam Nasiru Kabara Yayi Bajinta Kuma Yayi Aiki Tuƙuru Wajen Kafuwar Ɗariƙar Ƙadiriyya a Yammacin Afirka, Saidai Bayan Wafatinsa Babu Abunda Ɗariƙar ta Dinga Samu sai Naƙasu da Koma baya....
Izala Suna da Makarantu da Masallatai aƙalla 1000+ Banda University da Colleges a Nigeria..
Tijjaniyya Suna da Makarantu da Masallatai aƙalla 2000+ Banda University da Colleges a Nigeria.
Shi'a Suna da Makarantu da Masallatai aƙalla 500+ a Nigeria....
Abunda zai Baka Mamaki Wallahi Har Yanzu Ƙadirawa Basu da Masallatai da Makarantun da Suka Kai 2000 a Nigeria....
Idan Kaga ana Gina Masallaci ko Islamiyya In Allah ya Yarda Zaka Tarar Ƴan izalane ko Ƴan Tijjaniyya Babbar Lalacewar itace Babu ko University ko Colleges da Sunan Ƙadiriyya Duk Nigeria....
Ɗariƙar Ƙadiriyya Proffesor da Doctor ɗin ƴaƴan Wannan Gida Wallahi Basu da Yawa, Tijjaniyya Izala Shi'a Suna da Manya Manyan Ƴan boko Waɗanda Suke Basu Gudunmawa Zahiri da Baɗini, Ƙadirawa kuma babu Abunda suka iya sai Neman Rayuwakan Ƴan Uwansu.
Maulana Sheikh Sidi Musal Qasiyuni Kabara da Kansa Yake Cewa Ranar addu’ar ukun Mallam Kabara Talata 08/10/1996 , Shaikh Yusuf Makwarari R.A ya jagoranci daukacin Qadirawa sukayi caffa ga daukacin ‘ya ‘yan Malam a matsayin Halifofin sa, Ni kuma Al-Qasiyuni na ari bakin ‘yan uwana bada shawartar su ba na nada Qaribu a matsayin Halifan Malam.
Malam bai nada wani a matsayin Halifar sa ba; Allah ne shaida banyi haka ba sai dan asirin gidan ya rufu kan Qadirawa ya hadu, sai dai kaddara ta riga fata, wanda nayiwa bajintar bai godewa Allah ba , ya raba kawunan mu, ya tozarta gidan, har takai yau shine jagoran makiya a gidan wajen yiwa ƙanin mu ƙazafin zagin Shugaba (Waliyazubillah), Ni kuma yau shekara biyar yayi amfani da ‘yan daba da police ya hana ni gabatar da karatuka da tarukan Addini da nake gabatarwa a gidan , Karatun Asshifa kadai ya rage shima yayi iya yin sa Allah ne bai nufa ba.
Wannan bayani nayi shi ne don wanzar da gaskiya, ba don muzantawa ko kai kara ga wani mahluki ba.
Da Allah na dogara kuma gare shi nake kai kukana.
Abunda har yanzu Qaribu ya gaza fahimta shine Wallahi tallahi billahi zaman Kabara Lafiya Kasancewar Maulana Amirul Wa’izina (H) acikinta bawai a banza Sarkin yaqin ɗan fodiyo yayi masa Sarkin gida ba yaga abunda ya gani ne Allah ya haska masa sirrin gidan da gadon gidan yana tattare da Maulana Amirul Wa’izina (H)
Sun haɗa kai da Tsohon Mai Mulki Sun yaga sutturar da Allah ya dinka ma Amirul Wa'izina yanzu kuma Tshohon Shugaba zai fara kaskanta dan Allah ya janye wannan sirrin dake tattare dashi a daidai sanda Maulana Amirul Wa’izina zai fito cikin izza da buwaya fiye da wacce ake ciki.
Sirrin Kabara ya koma Gwale