Daga Wannan Litinin Kingin Kwanakki 161 Kubar Mulki..!!



* MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES *


Wannan haka yake, zamani yakan kawo abu in lokacinsa ya yi, kuma yakan kawar da shi in lokacinsa ya wuce.


Da, mata sunyi yayin wani Zani wai shi Maryam Abacha, da zamaninsa ya wuce sai ya zama tarihi. Yanzu Zanin da mata ke yayinsa shine A'isha Buhari.


Buhari ya dade yana neman mulkin farar Hula, kuma ya riqa shan kaye wajen Obasanjo, 'Yar Aduwa da kumà Good Luck.


Duk wannan abu ya faru ne sakamakon rashin zuwan zamaninsa.


Ba za ku fahince ni ba, dole sai kunyi nazari mai zurfi cikin wannan Hadisi da zan kawo shi a qasa insha Allah.


Manzon Allah (S.A.W.W) na cewa;

" WANI ZAMANI ZAI ZO WA AL'UMMATA, SHUGABANNINSU ZA SU KASANCE AKAN ZALUNCI, MALUMANSU KUMA AKAN HANDAMA DA QARANCIN GODIYA, MASU IBADUN CIKINSU KUWA AKAN RIYA (yin aiki ba don Allah ba), 'YAN KASUWARSU KUMA AKAN CIN RIBA DA BOYE AIBU CIKIN SAYE DA SAYARWARSU, MATAYENSU KUMA (will be busy with the ornament) AKAN QYALQYALIN DUNIYA, (duk sun zama 'yan iska rundunar Shaidan), TO, A WANNAN LOKACI SAI A 'DORA MUSU MAFI SHARRIN CIKINSU (yayi ta azabtar da su da nau'in azaba), ZABABBUN CIKINSU (irin su Sayyid) KUMA SUYI TA YIN KIRA (a kaucewa zalunci a dawo kan hanyar gaskiya) AMMA BA ZA A AMSA MUSU BA (sai 'yan kadan) ."


(Biharul-Anwar, J:23, Sh:22)


===== A YIWA KAI ADALCI ======

______________________________________


Idan ka duba shugabannin da ake da su ba abinda suke yi sai zaluntar talakawansu ta hanyar kisa ko kuma cinye musu dukiyoyinsu.


Ba za ka fahinci malamai ba sai harkar kudi ta taso, yanzu za kaga ana warwaso da gemu da Rawunna. Sannan yawan masallatai ma amsar wani abun ne.


Ya yanayin 'yan kasuwar garinku suke?

Matan da kuke mu'amala da su cikin gida da waje fa?

Wanne irin hali kuke ciki yanzu sakamakon Shugaban da zamaninku ya kawo muku?


Uhmm, kai dai kasan amsar da za ka bayar.


Daga wakilanmu na Zone din Bauchi, Gombe da Adamawa.


Tare da (Ado Isah Guda)


08137925034/08126385470

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post