Kiri Kiri yanzu an jirkita karya ita ce a matsayin gaskiya, ita gaskiya kuma ita ce a mazaunin karya, ana ta tafiya a haka kuma, duk da mun sani cewa watan wataran komin dadewa sai gaskiya ta yi nasara akan karya, amma dai gaskiyar na shan wahala a yanzu.
Su al'ummar kasar nan ka rasa irin tunaninsu ma, ka gaza gane shin wai su menene Hadafinsu , mun wayi gari malamai sun zama makwadaita maha'inta mabarnata yan' wawura, a lokaci guda su kuma al'umma din suna bin wadannan miyagun malaman da sunan su ne malamansu Jagoransu.
Ga al'umma har al'umma amma ba ta da Hadafi, kuma in dai dan ita ce sai ka ce ba ta da fata, fatan al'ummar nan har yanzu bai wuce idan zabe ya zo ba su fita su yi zabe, idan zabe ya kare su ci gaba da zama cikin zilla da kaskanci da kuncin rayuwa har zuwa wasu shekarun idan zabe ya zagayo su kara fita su yi wani zaben, shikenan fa ba su da wani tunani a kalla na cewa shin wai wannan zaben da suke yi tsawon shekarun nan da me suka amfana da shi, wane amfani suka samu babu wannan tunanin sam sam, ballantana kuma su yi tunanin jaraba mafita a addini.
A haka fa wannan al'ummar take rayuwa, rayuwa cikin kaskanci da wulakanci a karkashin tsarin zalunci da azzalumai, babu tunanin future din su a gaba da na ya'yansu da wasu generation ma su zuwa nan gaba, babu wannan a tunanin wannan al'umma din, wace irin al'umma ce wannan wadda bata san kan ta ba, ta sadaukar da kan ta da kan ta ga makiyanta macutanta azzalumanta, a lokaci guda kuma ba ta ma san ta yi hakan ba.
Wai yanzu mutane duk suna nan suna ta jira ne zabe yazo sai a samu canjin gwamnati shikenan sai komi ya yi tsaf, hatta ma ga wadanda aka takura ma wa a addini aka kama malaminsu aka tsare ko kuma aka hana su gabatar da komi su kawai tunaninsu shine ranar zabe su fita kwai da kwarkwata su zabi wata jam'iya ta nan ne za su samu yan' cin yin addini mai lasi, ka rasa irin wannan al'umma da muke rayuwa a cikinta.
Su yanzu azzaluman nan kenan Idan suka ga dama suna cin zabe sai su takura ma wani bangare na al'ummar da ba sa so har tsawon mulkinsu, sai idan karshen mulkin ya yi sai su kuma mutane su fito su canza gwamnati idan suka yi sa'a suka canja sai ita kuma wannan sabuwar gwamnati ta takura ma wasu bangaren iya tsawon shekarun mulkinsu, sai su yi ta hakuri har zuwa lokacin zabe sai a fito a kada gwamnati sai a takura wasu wadanda ba a so, wa to kenan a haka za ai ta tafiya babu ranar da ita kasar da al'ummar za ta canza ta zama abu guda kenan ko?
Wai wace irin al'umma ce wannan muke rayuwa a cikinta murdaddiya mara kan gado haka, al'ummar da ba ta tunanin gaban ta sai yau din ta, kullun ba ta da fata, hatta a addini ba ta da fata, ta manta ma addininta da Hadafinta. Alhali a lokaci guda wannan al'umma din Allah (T) bai barta haka kawai sakaka ba, sai da ya tayar mata da wanda idan ba ta bi sa ba akwai hujja akan ta, duk alamomi na karbar wannan hujja din sun cika cif, amma kuma har yanzu kamar ma basu san cewa Allah ya yi haka ba.
Muna fata Allah (T) ya kawo mana sauyi da sauki, ya taimaka mana, ya bamu juriya ya taimaki Jagora akan abinda yake kiran wannan al'umma a kai, ya sa mu daga cikin ma su karbawa mataimaka na gari, ya sa mu amfana.
Abba Salisu
17Dec2022.