Zalincin da Aka Yi was Shaikh Abduljabbar Constitution Ne Zai Ba Addinin Musulumci Dama? Ko Addinin Musulumci Ne Zai Bawa Construction Dama?


@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@


“A fahimci wannan maganar, ni ina magana da Musulmi ne ba ina magana da wanda ba Musulmi ba, da shi gwamna Ganduje da jama’arsa da ‘cabinet’ ɗinsa da malaman da su ka kai ƙara da alƙalin da ya yi hukunci da ma su sa ido su na faɗin ra’ayoyinsu; su na ke magana da su, ba ni magana da waɗanda ba musulmi ba tunda dama ƙila bai da addini ko kuma ‘constitution’ ɗin ya yi masa dai-dai ko bai da shara’a, bai da doka amma mu mu na da shara’a mu na da doka, asasan idan za mu gaya wa kammu gaskiya.


Dan har na ke cewa ba ni tsammanin Ganduje da jama’arsa da ma duk malaman da su ke sa baki su na goyon bayan mummunan hukuncin da aka yi wa Malam Abduljabbar na zalinci, ba na tsammanin gwanduje zai bayyana kamar yadda ni ke maganar nan yanzu a gaban talabijin ko rediyo da jama’arsa su zagaye shi su ce “Billahillazi La’Ilaha Illahuwa, wannan hukuncin da aka yi wa Malam Abduljabbar wurin Allah Karɓaɓɓe ne kuma an yi shi yadda Allah Ya ce ko lahira ba a sakewa”. Akwai wanda zai iya yin wannan? (babu) me ya sa ya san ba dai-dai ba ne, babu wanda zai yi gangancin yin wannan... 


Amma inda ace Al-ƙur’ani ne ke iko da ƙasar sai Malamai su ka haɗu su ka yi irin wannan hukunci ɗin, to su su na iya yin wannan rantsuwar saboda sai sun ƙure ƙoƙarinsu da iyakar iyawarsu sun tuntuɓi wanda za su tuntuɓa sun tabbatar da cewa bisa yaƙini ko mafi rinjayen zatonsu 60 bisa 100 abinda su ka yi dai-dai ne sannan sai su rantse... su ce ko lahira wannan hukuncin haka ya ke sai dai a tsarkake shi amma ya riga ya zartu. In banda haka nan ya Allah zai ce a yi? da babu dai-dai ɗin ya Allah zai ce a yi dai-dai ɗin? ba Allah Ya ce wanda ya yi kisa a kashe shi ba? wanda ya yi ridda a kasheshi ba? kaga akwai kenan.


Amma ba yadda za a yi Ganduje da jama’arsa su rantse (irin waccan rantsuwar, cewa hukuncin nan) ya gamsar da Allah gobe ƙiyama ba sai an sake ba. In kau sai an sake to su na cikin haɗari yanzu, wanda ke goya ma su baya ya na cikin haɗari, wanda ya sa baki ciki ya na ciki haɗari, wanda ya yanke hukuncin ya na cikin hadari, malaman da su ka kai ƙarar su na cikin haɗari in dai ba za su iya yin wannan rantsuwar ba to su na cikin haɗari tun duniya kafin a je lahira, abu na farko kenan.


Abu na biyu ‘Constitution' (tsarin mulkin Najeriya) ba ya da iko a kan Al-ƙur’ani, ba ya da iko a kan sunnah, ba ya da iko a kan Hadisan Manzon Allah dan bai da ruwa da shi. Ta yiwu wani ya ce to ai kotun musulunci ce. Sai mu ce ka tambaya ka ji kotun nan da ake cewa ta musulunci, in baka sani ba duk wani alƙali mai rawani ya na ƙarkashin Chief Justice (CJ) ne na jaha ko na ƙasa, (atoni janar na tarayya), wa ya kafa Chief Justice? shi ne ‘Constitution' saboda haka abinda ya gangaro daga Chief Justice ko ma minene ƙarƙashin tsarin mulkin ya gangaro hatta ko da an ce ma sa musulunci. In kau daga ƙarkashin ‘Constitution’ ya gangaro me zai maida shi na Musulunci kuma?


Misali: Ba mu na da ƙaton ita ce ba, kamar ɗorawa ko ɗunya ko kaɗanya manya-manya? Idan su ka daɗee a ƙasa har su kan yi kauci sai ka ga sun fitar da wani ganye ba banda wanda ke jikin reshensu, sai a ce kauci (Kaucin ɗunya ko na ɗorowa...). Ganye ne banban da wanda ke jikin itacen, to kamar haka ne waɗannan kotunan (da wai ake kira) na Musulunci su kamar kaucin ‘Constitution’ ne, ko alƙali wanene kau komin naɗinsa.


Saboda haka alƙalin musulunci na taka rawar kiɗan da Chief Justice ke yi ne. Chief Justice na kiɗa alƙali na rawa, wannan haka ya ke ba ɓoyayyen abu ba ne, ba wani sirri ba ne na ke faɗi na daban ba, abu ne haka ya ke rubuce. Saboda haka alƙalin musulunci a kotun musulunci da ya yanke wa wani musulmi hukuncin kisa saboda ya yi saɓo a cikin Musulunci to ‘constitution’ ne ya yanke ma sa hukunci a kan ya yi saɓo a cikin Musulunci wanda ba shi da wannan hurumin. 


Idan haka ne ka ga wannan hukuncin (na Abduljabar) bai da shar’iyya bai da hurumi. Alƙalin bai da hurumi, gwamnan bai da hurumi, ba wanda ke da hurumi domin:


 الإسلام يعلو ولا يعلى عليه.                   


“kullum Musulunci shi ke sama ba a hawa kan Musulunci”. Amma yanzu wa ke sama? Ana sama da Musulunci ne. Wa ke sama da shi? Shi ne; ‘Constitution’.


...كلمة الله هي العليا...و كلمة الكفر هي السفلى...    


Alkur’ani kalmatullahi ne, shi kuwa ‘constitution’ fa? to kar mu ce ma sa kalmatul kufuri wasu su ji ba su ji daɗi ba saboda su musulmi ne, kuma su na cikin al’amarin sai su ji babu daɗi kamar an  ce ma su kafurai, ba haka ba ne. To mu sassafta ma sa shi ‘Constitution’ ɗin ko mu ce ma sa son zuciya, ko mu ce ma sa zalunci, ko mu ce ma sa ɓata, ko mu ce ma sa halaka!! mai sauƙi-sauƙi za mu gaya ma sa. Amma idan mu ka ce kafirci sai wani ya damu saboda ya na mu’amala da shi amma idan aka ce ma sa zalinci ko ɓata ko son zuciya to ka ga duka kuma mu na iya bin Alkur'ani (mu ji me ya ce) dan ya warware mana wannan. Alal misali idan aka ce ma sa zalinci, Allah Ta’ala Ya ce: “wa ya fi zalinci irin wanda ya bar shiriyar Allah Ya bi son zuciyarsa”? ka ga azzalumi kenan. wani wuri kuma Allah (S.W.T) Ya ce: “kafirai su ne azzalumai”, to wazzalimuna kuma fa? humul kafiruna. Ka ga Ta mayar ta nane. 


To ka ga duk yadda mu ka kira shi dai-dai ne saboda duk ga shi ga matsayinsa. Shin cikin waɗannan (tsakanin son zuciya da kafirci) kuma, wannene dai-dai Musulmi ya yi? idan mutum ya yi miye ladarsa? idan an je aljanna, ina Aljannar son zuciya? ina aljannar halakakku? ina aljannar kafirai? ina aljannar ma su bin son zuciya? Idan za mu gaya wa kammu gaskiya maganar nan haka ta ke sai dai idan ba mu son gaskiya, musulunci daban, Najeriyanci (Constitution) daban”.


—Shaikh Yaƙub Yahya Katsina a wani ɓangare na jawabinsa kan mummunan hukuncin zalincin da aka yanke wa Shaikh Abduljabar Nasiru Kabara Kano. Yayi jawabin bayan kammala karatun juma’a (23/12/2022).


   #SYYK

26Dec2022

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post