@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
—Bilya Hamza Dass
Ko ƙaramin yaro ka tare a bisa hanya kace masa Dan Allah menene abinda ya kai sojoji gidan Mallam Zakzaky a gyallesu? ai kuwa za kaji yace maka sunje su kashe shi ne! Wannan magana zan iya akanta yin alwala na dafa Ƙur'ani na mai-maita cewa an aika sojoji gidan Mallam Zakzaky, domin su kashe shi ne kaitsaye! Kuma baku sani ba, wannan ba shi ne karo na farko ba, anyi haka akalla sau 10 a gajeren kari kenan. Sunyi tayin abinda ake ce masa niyya kan haka.
Ku tina yanda sojoji suka fita da Mallam Zakzaky, a gidan sa cikin yanayi marar tabbas! da kuma yanda lamarin yazo ya kaya, Ayace Allah Taala ya saukar me girman gaske, bana ce sun kashe Mallam Allah ya tayar shi ba, ba domin Allah baze iya ba sai domin ban sani ba ko anyi, ammade abinda nasani kuma kuka sani shi ne, idan aka cire Mallam Zakzaky, babu wani 'Dan Adam da ya rayu cikin tsakanin ikon Allah a tsakanin makiyan sa a wannan Nahiya da muke ciki idan akwai, nasan ni da ku bamu sani ba, ba ina takaita sanin ku bane, hujja nake kokarin baku.
Nisan kwanan Mallam Zakzaky ya tsiyata wasu ya lalata wasu ya haukata wasu ya kuma gargadi wasu sannan ya sanya wasu sun halkalta wasu kuma sunyi nadama wasu kuwa sukayi ƙara lalacewa! Me nake nufi? Ya tsiyata wasu akwai wanda yace idan Zakzaky ya rayu to shi Allah ya tsine masa! Kaga ai ya tsinantu ya kuma tsiyace ko? Wasu kuwa lalacewa sukayi a baya suna da Daraja sun zaci ta faru ta ƙare sai suka ta sakin baki akan Mallam Zakzaky, sai ta tabbata Mallam na nan sai suka lalace da ƙaskance a idon masoyan su wasu kuwa sai bayan sun sake ganin shi suna Hauka suna fade-fade da kaman mashaya.
Na san waɗanda kuma su kayi nadama suka shiga taitayin su sukayi dana sanin aikin su da kalomin su, bayan sun tabbatar da nisan kwanan Mallam Zakzaky, lalle wasu sunyi nadama suka hankalta. Taro guda kuwa lalacewa suka sakeyi! Babu mamaki idan kaji a tarihi cewa wasu kafurai suna tambayan suga aya domin suyi Imani amma idan an nuna musu Ayar sai suce ai wannan Sihiri ce! Su sake lalacewa su tsiyace duniya suyi nadama lahira. Nisan kwanan Mallam ya ƙara masa mabiyan da sauti be masa ba, Allah kenan!. Nisan kwanan Mallam ya jarabci masoya da maƙiyan sa. Musamman mu Masoya!.
Bamusan wani mutum da mace ta haifa wanda akayi masa abinda akayiwa Mallam Zakzaky kuma ya rayu ba, babu shi! Ina nema a fadamin idan akwai, babu!. Inada Aboki Kirista da naga yayi kwalla randa ya fara jin maganan Mallam bayan yafara magana da masu jarida yace wannan ko de Mala'ika ne? Tsabar tsananin mamakin Nisan kwana da hakuri gami da tawakalin Mallam. Ta isa masifa ga bawa da karshen jarrabawa kazama cikin masoyan Mallam ba ma fa mabiyi ba, just comon masoyi! to balle!
Wa aka harba sama da 5 a jiki kuma ya rayu? ba kawai jiki ba a'a wajaje masu hadari irin su kayi, Ido, ciki da sauran su! Wannan nisan kwana gaskiya ba hakanan ba kawai! Allah yana nufin Mallam da wani al'amari, mene al'amarin? Bansani ba amma ina iya hasashe, Allah yana nufin tabbatar da Addini a wannan nahiya da wannan kasa tamu da muka dade muna kishin haka, kuma ya nuna wa Mallam haka tin shekaru 40 baya, sannan ya kaddara zai haifar da haka tare dashi, wannan hakane.
Shiyasa Mallam yaƙi sarewa Allah kuma yaki yabar dafa masa! Allah yaso Mallam, Mallam yaso Allah, Allah ya yarda da Mallam, Mallam ya yarda Allah. Duk tarin maƙiya sai anyi lamarin nan, haka duk karancin mabiya sai anyi lamarin nan, ya rage ga kowa yaga yaya za'ayi zezo ayi dashi ko ze tsaya kallo, ko kuma zai hana ayi ne? Mallam muna nan tare dakai ko zamu rasa komai ciki kuwa harda Uwa da Uba karshe kenan! Allah Ya Tabbatar damu....