Yan shi'a suna karyar son Manzon Allah (S) ne, saboda suna goyon bayan shaik Abdul jabbar akan zagin Annabi (S) da yayi...!

 



@ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@


Wannan magana ta fito daga bakin wani malami ne, to sai nace masa, mu yan shi'a bamu bayarda shaik Abdul jabbar ya zagi Annabi (S) ba.

Saboda mu muna bin wasiyyar Manzon Allah (S) ne, da yace ya bar mana Alkur'ani da Ahlil baity a bayansa, saboda haka idan aka zo mana da labari, za mubi alkur'ani ne wajen karbar labarin.

,

Allah yace,


 يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنْ جَاءَكُمْ فَاسِقٌ بِنَبَإٍ فَتَبَيَّنُوا أَنْ تُصِيبُوا قَوْمًا بِجَهَالَةٍ فَتُصْبِحُوا عَلَىٰ مَا فَعَلْتُمْ نَادِمِينَ 

Yaku wadanda suka yi imani idan fasiki ya zo muku da labari, kuyi bincike, don kada ku cuci wasu mutane bisa jahilci, sai ku wayi gari kuna nadamar abinda kuka aikata.

,

To kun yanyanko karatun shaik Abdul jabbar na minti 5 acikin karatun awanni kuce ya zagi Annabi (S) sai mu yarda, baza mu bincika ba? Dole mubi alkur'ni mu bincika, mun nemi cikakkun karatutunsa da suka daddatso, mun saurara daga farko har karshe, mun tabbatar bai zagi Annabi (S) ba, yana ma kare shi daga miyagun hadisan da suka ci mutuncinsa. 


Ga misalin hadisi daya da Abdul jabbar yayi bayani akanshi, hadisin da sukace wai Annabi (S) yana kewaye matansa 11 da jima'i dare da rana. Kuma suka ruwaito cewa idan yaga mace ta wuce sai saha'awar sa ta motsa, sai ya tafi gida ya biya bukatarsa.

Game da wannan ne sai Shaik Abdul jabbar ya kore wannan hadisin akan Annabi (S) har yace sun mayar da Annabi (S) kamar bunsuru.


To sai suka ce ya nuna kalmar bunsuru acikin hadisin, to ai shi yayi misali ne yadda aka siffata Annabi (S) a wannan hadisin, ba yace shine bunsurun ba. 

kuma ko wana malami yana irin wannan.


Ga misalin daya, dan gidan gumi ya karanto hadisin da manzon Allah (S) yace, a kawo masa abin rubutu na rubuta muku abinda idan kuka yi riko dashi, baza ku bata, umar bin khaddab ya hana yace littafin Allah ya ishe su.

Dan gidan gumi yace abinda hadisin yake fahimtarwa shine da ba dan umar ya hana Annabi (S) yin rubutun nan ba, da Annab i(S) ya rusa musulunci, da yin rubutun nan, wannan ba cin mutuncin Annabi (S) bane? Dan me ba a kai dan gidan gumi kotun musulunci ba, ya nuna kalmar Annabi (S) zai rusa musulunci idan yayi rubutun nan a cikin.hadisin, idan bai nuna ba a yanke masa hukuncin kisa.


Mun fahimci cewa matsalar Shaik Abdul jabbar siyasa ce, da kiyayya da hassada daga cikin wasu yan uwansa, suke kokarin kashe shi, shaik Abdul jabbar shi yake da gaskiya akan wannan case din.


Mu kuma da yake kur'ani muke bi Allah yace,

 يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَكُونُوا مَعَ الصَّادِقِينَ

Yaku wadanda suka yi imani kuji tsoron Allah ku kasance tare da masu gaskiya.

Baza mubi son zuciyar wasu ba, mu goyi bayan zalinci da ta'addanci ba, saboda munyi imani da Allah da mazonsa da ranar hisabi.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post