Yakamata ku fahimci kawaicin mu.!!!

 


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


A mimbari kuma du, Marigayi Sheikh Albani Zariya ya kirayi Sahabbai ƴan Daba, masu zuwa Kulub, baku kwabeshi ba, ba kuyi Allah wadai da kalaman sa ba, saima kuka hau sharhi a mutane cewa mune bamu fahimci bayanansa ba, bayan da harshen Hausa yake magana.


A mimbari Marigayi Sheikh Jafar Mahmoud Adam ya kira Annabi kamar Envelope ta wasika, yace menene amfanin Envelope in an zare wasika? to mu dauki wasikar, shine Kur'ani, mu ajiye Envelope a gefe, baku tsane shi ba, baku kyareshi ba, baku ce a kasheshi ba, shima sai sharhi kukai ta mana akan bamu fahimce shi bane.


A mimbari Sheikh Gero Argungu, yai tatas a Iyayen Annabi, a kokarinsa na rushe tawassuli, yace mutumin da ba'a san yadda tsofinsa 🥺 (Iyayen Annabi kenan) Astagfirullah suka ƙare ba, yai wasu kalaman da ba zan iya furtasu ba, maimakon wani ya daka masa tsawa akan rashin ladabin da yaiwa Sayyidi Abdullahi da Nana Aminatu, sai ma aka rude da kabbara, ba kuce a kashe shi ba, baku halasta jininsa ba.


Amma mu a wannan kafar ta Soshiyal midiya, mun sa tukwuicin Miliyan 10, duk wadda ya kawo jawabin wani Malamin Shi'a a Nijeriya da ya zagi Sahhabi ko Iyayen Annabi, ko da misalin irin zagin da muka lissafo maluman dake kiran kansu Sunnah ne suka yi, yazo ya amsa, har zuwa yanzun nan ba wadda yaci Kuɗin.


Saboda rashin ta ido, da rashin Albarka, zaku ce wai Malam Abduljabbar ya zagi Annabi, aje a kashe shi? Yanzu da za'a ce Buhari da Muslimu sun kasance suna zuwa gidan wata mata ta cire musu kwarkwata akai, ko suna fitsari a tsaye akan Bola, ko ace Iyayen Sahabbai ƴan wuta ne, sai kun jijjiga Nijeriya da ihu akan mimbari ranar Juma'a, tunda gwamnatin ta kuce kuce an zagi Iyayen Sahabbai, amma da yake akan Annabi aka ruwaito hadisan, kunyi lakwas da kawuka, ai daidai ne, hadisan ma sun inganta. 


 Sannu dangin Banu-Umayyah, ai ko a Mulkin Abbasiyawa ne, wannan rashin lissafin naku Albarka, kawai kuce kuna da Gwamnati, zaku kashe Malam Abduljabbar saboda yana warware ruwayoyin ƙarya da aka jingina ma Annabi, ku kuma hakan kashe muku kasuwa ne wajan yaki gidan Annabta, Faqat.


Kuda kuke da Gwamna, Shugaban ƙasa, ƴan Majalisu da kotu, kuje kuyi kisan kamar yadda kuka saba, ai kunyi a Zariya, an muku wani abu ne?, cewa kawai mu kayi Allah zai isar mana, to mene sai kun haɗa da sharri akan abinda kuna da karfin zartawar akai, ikone dai baku da shi, sai Allah yaso Malam Abduljabbar zai mutu, ai ta bala'in makircin, ƙarshe dai zai kubuta Insha-Allah, kamar Annabi Musa a gidan Fir'auna. 


Gaskiya ba'a rusata da bindiga. 


Muhd Bala Afuwa

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post