Wannan ita ce hirar da wakilinmu ya yi da matar Malam Abdullahi Abbas, Malama Zainab wacce ta rasa 'ya'yanta 6 da kuma Maigidanta a Gyallesu bayan Sojojin Nijeriya sun kai harin ba gaira ba dalili a muhallin a ranar Asabar zuwa Lahadin 12-13 ga watan Disamban, 2015. Tun daga wannan hari da Sojojin suka kai suka kashe Dubban mabiya Malam Zakzaky, har ya zuwa hada wannan rahoto babu takamaiman labarin inda 'ya'yan na ta da maigidanta suke. Sai dai wata majiya tabbatacciya ta tabbatar da shahadar Maigidanta Malam Abdullahi Abbas.


Ga hirar kamar yadda take:

ALMIZAN: Da farko zamu ki gabatar da kan ki ga masu karatunmu?


Malama Zainab: Sunana Zainab....

ALMIZAN: Bayan harin da Sojojin Nijeriya suka kai a tsakananin Husainiyya da Gyallesu, zamu so mu ji ko mutum nawa ne ake da tabbacin shahadarsu kuma mutum nawa har ya zuwa yanzu babu labarinsu a wannan gidan?     


Malama Zainab: mu dai ana ta bamu labarin wannan ya yi shahada, wannan ya yi shahada, mu kuma ana dai fada mana tunda bamu tabbatar ba, ba a kuma bamu gawar ko daya ba, ba a bamu gawar ko daya ba. Don haka dai ana cewa kamar ko mutum Uku (3) ne aka ce sun yi shahada, amma kuma har yau bamu gawar ko daya ba.

Muna dai sa ran ko da rauni ne ko shahadar ne ko a raye ne, duk abin da Allah ya tabbatar kawai shi ne daidai. Domin shi Allah da yake tare da kai, shi ya fi kowa son ka. Don haka duk abin da ya faru mun san jarabawa ne daga Allah. Muna dai rokon Allah dai ya tabbatar damu.


ALMIZAN: zamu so mu ji adadin mutanen da aka rasa a wannan gidan?

Malama Zainab: akwai Abdullahi Abbas (Maigidana), sai Abdurrazak Abdullahi, Abbas Abbdullahi, Muhammad Abdullahi, Ahmad Abdullahi, Ibrahim Abdullahi, Jawad Abdullahi.

 
'ya'yanta shida da ta rasa tare da maigidanta

ALMIZAN: zamu so ki yiwa masu karatunmu bayani, cikin wadannan mutum 7 da aka rasa a wannan gidan, 'ya'yanki nawa ne a ciki?


Malama Zainab: duka wadannan da aka rasa, duka nawa ne ('ya'ya 6) sai kuma Maigidana.

ALMIZAN: ya zuwa yanzu babu wani takamaiman labari da kuka samu dangane da ko an kashe su ko suna raye?

Malama Zainab: babu takamaimai, mu dai ana gaya mana, wannan ya yi shahada, wannan ya yi shahada. Mu dai muna sa rai, idan ma sun yi shahada, Allah ya karbi shahadarsu, idan kuma suna nan, Allah yasa wani aikin ne ya rage da za su karasa.

ALMIZAN: zamu so ki yi mana bayanin yadda kika rabu da su su 7 din ko da a takaice ne?

Malama Zainab: da yake duk suna makaranta ne, ba wanda na yi magana da shi.

ALMIZAN: ya ku ka ga wannan waki'a da ta auku?

Malama Zainab: lallai wannan jarabawa ce mai girma daga Allah, kuma dama hanyar ke nan. Sannan sama su Yaran nan suna fada cewa; su ma'aikata ne, idan lokacinsu ya yi za su tafi (idan suka kammala aikin su).

ALMIZAN: da yake a lokacin da Sojojin nan suka kai hari a Gyallesu, ta kaima har an kama jagoran wannan tafiya, Malam Ibraheem Zakzaky tare da karin kashe 'ya'yansa guda Uku da harbin matarsa sannan shi kan shi Malam an harbe shi, ya kuka ji wannan labarin? Ganin cewa kema kin rasa 'ya'ya 6 da Maigidan ki?

Malama Zainab: ni babban abin da yake kara tayar min da hankalina shi ne; karin shahadar 'ya'yan Malam Uku, wanda wannan yasa yanzu har hawan jini na ya tashi (cikin kuka ta yi maganar).

ALMIZAN: zamu so mu ji halayyar wadannan 'ya'yan na ki da kika rasa?

A yayin ganawarta da wakilinmu a gidanta.
Malama Zainab: ni tunda nake tare da wadannan Yaran, basa kaunar bacin raina, nima bana kaunar bacin ransu ko kadan. Kuma duk gaba dayansu ba ni da matsala da su. Sannan kowa na tsaye da karatunsa. Kuma ba su son bacin ran mahaifinsu, haka zalika ba su son bacin raina har Allah ya raba mu da su, da fatan idan Allah yasa sun yi shahada. Allah ya karbi shahadarsu, idan kuma suna raye, Allah ya fito da su.

ALMIZAN: Abu na kusa da karshe wani sako kike da shi ga sauran 'yan uwa da iyaye irin ki da suka rasa suma 'ya'yansu?

Malama Zainab: abin da zance ga wannan iyayen shi ne; Allah ya kara musu hakuri da dangana. Tunda jagoranmu ma ga abin da aka yi masa fiye da namu. Wanda dansa daya ya fi namu wajen goma. Dan Malam kwara daya ya fi namu goma.

ALMIZAN: A karshe wani sako kike da shi ga 'yan uwa a wannan hali da ake ciki na babban jarabawa?

Malama Zainab: sako na shi ne wannan neman tabbata da sabati zamu nema. Allah ya bamu sabati da tabbata da juriya.