Waye waliyin Shin wanda aka ce za'a kashe yake dariya ko kuma wanda aka ƙwacewa mulkin duniya yake kuka?



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Shin ina hankali ?

Ka taɓa gani wanda ya ci mutuncin Annabi rayuwar sa na kya?


Shin ka taɓa ganin wanda yake yi don duniya baya tsoron mutuwa ?


Indai ba Wiwi kake sha ba, kuma ba duhun jahilci ke damun ka ba da cutar kwalarar ƙungiyanci ba zai yuwu ace Me zagin Annabi yafi ko wanne malami wayyayun mabiya waɗanda zukatansu ke cike da Ƙaunar farin jakada( S.A.W).

A yau kaf Afrika babu wanda ya tsaya yayi kira sannan yayi nasarar da har gwamnati ke masa hassada, sai Sadauki ikon Allah !

Bashi da sarki, bashi da gobna, bashi da alƙalai, bashi da masu kuɗi sai zunzurutun talakawa waɗanda suka narke a janibin shugaba. Amma a yau gabas da yamma kudu da arewa babu inda ƙarajin sa be jeba. 

Ya kai me karatu ka nazarci tarihin shugaba

 ( S.A.W) ka gangaro izuwa sayyadi Ali, sannan kayi ƙoƙarin sannin waye Umar bin abdul-aziz, to sai kayi la'akari da me ke faruwa akan Sheikh Abduljabbar, indai kaba ƙwaƙwalwar ka 'yanci to wallahi zaka fahimci haƙikar da muke faɗa maka.

In ma baka san addini ba, sai boko. To yi bincike akan tarihin 'yan gwagwarmaya na duniya kamar ;

Nelson Mandela, Martin Luther King, Mahatma Ghandi, John F Kennedy. Da dai sauransu, zaka gane duk wata gwagwarmaya na cike da mugun ƙalubale, Misali, saida Mandela ya ƙare rabin rayuwar sa a Prison ( Robin island) saboda ganin cewa wai shi ɗan ta'adda ne, amma daga ƙarshe sai da a kasar (S.A) ake kira shi da " Madiba" ma'ana uban ƙasa( father of the nation) kuma ya shugabanci ƙasar.

Don haka muna faɗin cewa Inshallah sai Musulmin Afrika sun watsar da hadissan ƙarya, da suka haifar mana da matsalar a musulunci, Fatan mu Allah ya fito da jagoran mu 🤲🤲🤲

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post