[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Gaskiyar Yadda Zancan ya ke!
Wallahi Tallahi da za mu buɗe babin Naƙadi da Naƙasha wasu mas'alolin da Sheikh Abduljabbar Kabara (H) ya tafi akansu da ansha mamaki ƙwarai ! Da sai an fara tambaya anya kuwa mu ɗin ne ? Da sai da yawan waɗanda muka tsaya sahu ɗaya dasu wajen bashi kariya sun zare kansakalin yaƙa rmu cikin naƙadi da munaƙashar wasu ra'ayoyi , matsaya , matafiya ta Sheik ɗin .
To amma gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata , hakan bazai hana mu kasance tare dashi akan wannan gaɓar ba , domin an zalunce shi, ba'a yi masa adalci ba , abinda ake yi masa Siyasar Addini , Siyasar Family da Siyasar jam'iyya da Mahukunta da Jahilci da wautar game garin mutane ne suka haɗu suke yaƙarsa dan suga bayansa , wannan wata gaskiya ce da ba mai musata sai mai son zuciya ko wanda ya jahilci abun da yake faruwa .
Muna ƙara faɗa muna maimaitawa game da matsayar akan wannan dambarwar itace :
1. Sheik Abduljabbar Masoyin Manzon Allah ne da iyalan gidansa , kuma mai basu kariya ne .
2 . Sheik Abduljabbar bai zagi Annabi(saww) ba , kuma baya nufin aikata haka ko da wasa .
3 . Sheikh Abduljabbar Mutum ne mai Ikhlasi kuma duk abinda yake yi yanayinsa da kyakkyawar niyya , cika ta Allah ce .
4 . Abunda yake faruwa dashi Siyasoshi ne da makirci da lauje cikin naɗi na ɓangarori mabanbanta da kowanensu yake da wata buƙata ta musamman a cikin haɗakar cutar dashi , koma ganin bayansa baki ɗaya .
5. Muna tare dashi saboda gaskiyar sa da kasancewar sa abun zalunta (Mazlumi) , da kuma al'amarin adalci wanda ko da Bawahabiye ko Kirista muka ga an yiwa haka za mu fito mu faɗi gaskiya ba ruwan mu , gaskiya da adalci muke kallo ba mutum ba .
Kowa yasan mukan bayyana irin zalunci da danniyar da ake yiwa Falasɗinawa, kuma muna goyon bayansu tare da tausaya musu , bare kuma Sheikh Abduljabbar Kabara (H) da bayan Addini , Mutumtaka da ƙasa ɗaya , uwa uba soyayya da wilayar Ahlul Baiti (a.s.) ta haɗamu dashi , wacce itace jigon da yasha gaban komai da ka iya haɗa mu .
Banda wannan bamu da wani abu a cikin wannan al'amarin , kuma ba ma neman komai gurin kowa , Ɗan Shi'a da Karantarwar Shi'a sunyi cikar da tafi ƙarfin ta nemi wani abu a wajen wani sai dai wani ya nema a wajenta .
فمالي إلا آل أحمد شيعة وما لي إلا مذهب الحق مذهب
#YA JABBARU KA TAIMAKI ABDULJABBARI 🤲
✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey