[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Ya Ɗan Baffana ina maka Wasiya na farko kayi aure, abayana , domin ba makawa ga namiji ya zamo yanada iyali (Ina maka Wasiya kada ka zauna bayan Shahada na kace baza kayi aure ba.
Sannan ina maka wasiya kada wani daga cikin wadannan mutanan da suka zalince ni su shedi jana'izana, domin su makiyana ne makiya Manzon Allah (S), kuma kada kabar wani daga cikin su yayimun sallah, ko daga cikin mabiyansu,(kada wani yayi sallah akaina) , Sannan ka birneni cikin dare , a lokacin da idanduna suka nutsu (wato lokacin da mutane suke bacci), a lokacin nakeso ka birneni ba tare da sanin wadannan mutane da suka zalince ba ko mabiyansu.
Sai ta cigaba da cewa Ya 'Dan Baffana idan na cika kamun wanka da kanka,Amma kada ka yaye suturata saboda ni tsarkakakkiya ce, kuma Tahaniki da sauran abinda akawa babana (Manzon Allah (S) Tahaniki dashi , Sannan kuma kamun Sallah.
Sannan wanda suke makusanta na iyalan gidana suyi mun Sallah tare dakai, kuma ka birne ni a cikin dare ba da rana ba. Sannan ka birneni a boye ba a bayyanaba ,kuma ka boye ƙabarina, Sannan kada ka shedawa wani jana'izana daga daya daga cikin wadanda suka zalince ni.
Sayyida Zahra (As) ta cigaba da cewa Ya Abal Hassan kada a daga murya ga yayana Wato Imam Hassan da Imam Hussaini, a tausaya musu kar a kuntata musu saboda jiya suka rasa kakansu Manzon Rahama (S) a yau kuma zasu rasa Mahaifiyarsu, idan har aka daga musu murya maraici zai kamasu.
A cikin Jawabin Sheikh Adamu Tsoho Jos na Zaman Juyayin Shahadar Sayyida Zahra (As) Wanda aka gabatar a Yau Talata 27/12/2022.
#HSZJ