@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
Mijin da ya kamata a Aura shine wanda ya haɗa suffofi guda shida '5'
1. SUFFA ta farko ya zamto yana da ADDINI. Wato musulmi ne kuma yana da tarbiyya ta addini. Dole a binkita domin addini yana da tasiri sosai wajen auratayya.
Toh Meye addinin? Shine mutum ya zama yana da suffofi guda 5 kamar haka:
- Idan Allah yace ayi, yana yi
- Idan Allah yace abari, yana bari
- In Allah ya bashi, yana godiya.
- Idan ya rasa abu, yana haƙuri
- In yai zunubi yana tuba.
Wannan sune suffofin mai addini na zahiri.
2)- Suffa ta biyu ya zamto yana da HALAYE MASU KYAU. wato ya zamto namiji Mai Mutunci, mai tausayi, mai girmama nagaba, yana da tausayin naƙasa, yana da kyauta, yana da alkhairi, yana da kishi. Dade duk suffofin da ake son Miji ya zamo yana dasu kamar su tsafta da iya magana don ƙara ingancin aure.
3. Suffa ta uku ya zamto ME LAFIYA. Wato kada ta zamto yana da wani ciwo, ko wata larura (naqasa) da zata iya hana sa kula da kansa ko kula da Matarsa, ko wani ciwo da zai iya yaɗuwa daga garesa zuwa ga Matar ko ga ƴaƴan da zasu haifa agaba, kamar irinsu (kanjamau, kwayoyin cutar sickler, ciwon hanta, da sauran su), don haka dole a tabbatar da lafiyar sa.
4)- Suffa ta huɗu ya zamto yana da SANA'A. Wato ya zamto yana da aikin yi. Ba ana nufin dole ya zamto mai kuɗi ba.... A'ah! Amma de ya zamto kwai wani abu da yake domin samun abinda zai Ɗan rufawa kansa asiri.
Domin munji hatta cikin annabawan Allah basu rayu haka ba kara zube, annabi dauda (AS) yana ƙira, Annabi Muhammad (SAW) makiyayi ne, Annabi Idris maɗinki ne, Haka har kan sahabbai.
Mun kuma ji yadda Manzon Allah (SAW) ya hana FAƊIMATU BINT QAYS ta auri wani Sahabi a lokacin da bashi da hali. Don haka dole a samu mutum me hali, me Sana'a da yake da abin yi komi kankantarta. Saboda inma babu toh komi soyayya sai an rabu wataran. Ka auri me zuciyar nema yafi ka auri me kudi. Wani yana da kuɗin amma baida zuciya, shima bai ci ba ballantana wani yaci.
5)- Suffa ta biyar ya zamto ME ASALI.
Wato asan asalin sa daga ina yake?
- Su waye iyayensa
- Su waye danginsa,
- Su waye yan uwansa,
- Su waye masu faɗamasa yaji
- Ya mu'amalarsa da duk waɗannan ɗin. Duk wajibi a sani.
Domin sau tari in matsala ta taso Mace ta kawo qara in akace kije ki gayawa dangin shi. Sai kaji tace ai shi baya jin maganar kowa, yafi karfin kowa, baya sauraren kowa, baya ganin kowa da gashi, baya ganin ƙimar kowa. To irin wannan ake gudu.
Domin wanda bashi da mafaɗi in larura ta taso saika rasa to waye zaka fadawa wanda zai masa magana, ko wanda zaku je a tattauna ai sulhu. Ballantana kuma ace Mace Marainiya ce dama.
6)- Suffa ta karshe wato ta shida shine ya zamto mutum ne me Kazar-Kazar, mai kai komo tare da fafutuka. Wato mutum ne da ansan in aka bashi aure zai rike koda yaya. Zai rike matar, zai ga mutuncinta, zai darajar iyayenta, da nasa iyayen. Bashi da Zage-zage.
--------------------------------------------------------------------
Toh tabbas idan aka sami wadannan suffofin shida sun haɗu a zahiri ga Namini toh abinda ya rage kurum ayi ISTIKHARA abashi Mata, ko kuwa Mace ta amsa masa. Insha Allahu baza aji kunya ba.
Addininsa, mutuncinsa, lafiyarsa, kyawawan halayensa, asalinsa, fafutukarsa, Sana'ar sa, hakan zai sa bazai abinda zai bada kunya ba. Zai rike yarinya da mutunci ko bayan ran Mahaifanta, sannan wani dalili tsufa ko Sabani, ko idan kanta ya qare, ko quruciyarta ta qare, toh bazai sa ya saketa ko ya wulakantata ba, ko yace zai watsar da ita.
____________________________________________________________________________
YAYA AKE NEMAN AURE?
Ma'ana taya Mutum zai ga Mace yace yana so, ko ta yaya Mace zata ga Namiji tace tana so.
Hanyoyin da ake bi wanda suka tabbata ko suke da hujja a musulunci guda 5 ne:
1. Hanya ta farko shine wani ya haɗa wata da wani da yake tunanin sun dace. Kamar yadda KHAULAT BIN HAKIM tazo ta sami ANNABI (SAW) Bayan wafatin Nana khadija (RA) tazo ta samesa tace ya rasulillah gashi khadija ta rasu amma akwai Mata guda biyu dana hango ma, daya bazawara, ɗaya budurwa. Kuma kowacce da akwai abinda na hango yasa nace ka aure su.
Ita wannan budurwar yar amininka ce, Babban abokinka Abubakar Sadik (Aisha), ita kuma Bazawarar (Saudat) Musulunta tayi mijinta kuma SAFARANU ya rasu. Idan ta koma gun dangi ko yan uwa zasu fitineta ko imaninta ya raurawa, shiyasa nake so ka aure su kuma yai hakan. To anan zamu ga ba laifi bane wani ya zamo mai dalilin aure in yaga wanda suka dace da juna.
2. Uba na iya nemawa yarsa Miji. Kamar yadda muka ji sayyadina Umar ya fita yana nemawa yarsa Hafsat aure gurin sayyadina Abubakar (RA) da sayyadina Usman (RA) wanda duk basu amince ba, karshe Manzon ALLAH (SAW) ya fito ya aure ta.
Don haka hujja anan Uba na iya bijirar da yarsa ga mutanen kirki, ba abin kunya bane, ba neman kai da ita bane, ba rashin sanin darajar ta bane, babu ruwanka da zamani kome mutane zasu ce, wayewa har gaban gobe tana cikin musulunci. Hasali ma haka ne darajar ta, ka tallata me daraja zuwa ga masu daraja.
3- Ko kuma Macen da kanta taga wanda take so da kanta. Tana da yanci ta bayyana masa cewa na ganka kuma ina sonka, ina kaunar ka, inkana sona shikenan, inbaka so na bakomi dama nice na hango sannan ba laifi kayi ba don bakasona, nima ba laifi nayi ba don ina sonka. Wannan ya faru ga Matar da tazo gaban Manzon Allah (SAW) take cewa ya rasulillah, inkana sona na baka kaina ka aureni. Wanda annabi (SAW) bai ce mata wannan kinyi abinda bai dace ba, ko kuwa kinyi abin kunya. Don haka wannan hanya ce ta uku.
Mace na iya sa Akira Mata mutum ta furta masa, ko tanemi lambar wayar sa ayanzu, ko ta tura masa a wasika, kota hanyar abokan sa, Kota hanyar Mahaifanta su su samesa Kota hanyar tura kawarta ko kanwarta ko ita kanta.
4- Namijin shi da kansa yaga Mace yace yana sonta. Kamar yadda JABIR BIN ABDULLAHI ke cewa idan ina son Mace na kansance ina maqalewa jikin bishiya don inga abinda ya kwanta mun arai, idan ina son sai in fito in bayyana mata. Hakanan sayyadina Abubakar da Umar duk sun zo sun sami ANNABI (SAW) suka ce suna neman Auren Fatima (RA) Amma Annabi bai amsa musu ba, da sayyadina Ali ya fito yace yana so sai ya amsa masa. Don haka ba laifi namiji ma yaje ya Sami Mahaifin Mace ya bayyana masa yana son yarsa da aure inya amince.
Wanda anan ne galibin Matsalar da muke samu kan fara, mukan je kurum mu haɗu da Mace irin haɗuwa ta bariki daga ganin Mace a hanya baka san Matar aure bace, ko budurwa, ko yar waye ba... Kurum ka hau mata ishara, wani ma tace musu ni matar aure ce kaji mutum yace to in matar aure ce sai me? Toh wannan yana da hatsari ba hanyar neman aure bace. Amma ba laifi bane, ka tambayi Mace ta baka lambar gidansu kaje ka sami iyayenta ku gaisa ka isar da kanka sannan kayi binkice. Kamata yai ma ai binkicen asibiti kafin nan, tun kafin magana tai nisa.
______________________________________
YADDA KUMA AKE BINKICEN SHINE:
Idan mutum yaje ya sami iyayen yarinya ya gabatar da kansa sai yace naga wance yarka inasonta da aure inbakai Mata miji ba, kuma nima ina so kai Binkice kaina. Kuma ka bani izini da izininka inzo gidan. Bawai yarinya ce ya kamata ta kawo gidan ba. A'a kamata yai kai da kanka kazo tun bayan da kaganta walau a makaranta, ko wani gu ka tuntuba kaji bata da aure.
5- Wani ya haɗa wata da wani. Koda wannan mutanen basu san juna ba. Ana farko can abaya Mace ce zamuji ta haɗa auren. Toh anan kuma namiji ne yake ganin dacewar wasu. Kamar yadda IBN QAYYUM ya kawo a littafinsa cikin wasu tabi'ai da suka haɗa wata mata da wani mutum wanda suka ce kai aiko halin su yazo daya da za'a hadasu da anga abin mamaki.
______________________________________
Don haka wannan sune hanyoyi 5 da aka samu a musulunci ko a tarihi da za'a iya hada aure. Hakanan duk wanda ya bayyanawa daya yana sonsa toh sai yace bani address zanje nai binkice akai, inya so daga baya sai kaji matsayata ko kiji matsayata.
Saboda kada sai daga baya kuma Mutum yaji ko yaga wani abu wanda zai kawo matsala. Duk ana yi ne don kare mutunci, kar aje sai angama shashanci, ko anyi ciki, ko anzubar da ciki, azo ace za ai aure ko wani abu, auren ma bazai kargo ba. Allah Yasa A dace.
Tags:
Taskar Ma'aurata