..El-Misawyy..
A Rana ta 12 Zuwa 14 Ga watan Disambar 2015 Sojojin Nigeria Sun yi Amfani Da Karfi Fiye da Kima Akan 'Yan Shi'a a Garin Zaria, yayinda Suka yi Kisan kare Dangi akan 'Yan uwa Maza da Mata, Jarirai Da Manya.
Wannan Yarinya mai karancin Shekaru, Batula Buhari Jega, ta rasa Rayuwarta ne yayin Harin Ta'addancin Da Sojojin Nigeria Suka Aiwatar Akan 'Yan Shi'a, yayin Harin Ta'addancin Yarinyar Ta Rasa iyayenta(Babanta Da Mamanta) suna daga Cikin Wadanda Sojojin Nigeria Suka kashe a Harin.
Tabbas Ranar Sojojin Sun Shekar da Jinane, Sun yi Kisan kiyashi tamkar a Filin Yaqi, Sannan Sun yi Kisan kai na Rashin Tausayi da Rashin Imani Akan Wadanda Basu da Ko Allura a hannunsu da Sunan makami.
Wannan Zalunci Mafi Girma, zalunci mafi Muni, zalunci ne da duniya ba zata taba Mantawa da shi ba.
Muna Rokon Allah ta'ala ya Daukar Mana Fansa, yayi Mana Sakayya da Gaggawa.