[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
-Wata Rana Sai Mutuminnan Ya Cewa lmam Ali (AS): "Ya Imam Shin Wai Menene Yasa Kake Saurin Bada Amsa da Zarar An Tambayeka, Me Yasa Baka Tsayawa Ka Shirya Ko Kuma Kayi Dogon Tunani Kafin Ka Bada Amsa???
-Sai Maulana Imam Ali (AS) Ya Tambayi Mutumin Cewa: Shin Kai 'Yan Yatsu Nawa Ne A Hannunka?
-Sai Mutumin da Sauri Yace: 'Yan Yatsuna Biyar Ne.
-Sai Imam Ali (AS) Yace Masa: Menene Yasa Baka Tsaya Dogon Tunani Ba Kafin Ka Bani Amsa?
-Sai Mutumin Yace: Ya Imam! Menene Yasa Zan Tsaya Dogon Tunani Akan Wannan Amsar, Alhali Nasan 'Yan Yatsuna Suna Gaban ldona Kullum lna Kallonsu?
-Sai Imam Ali (AS) Yace Kamar Yadda 'Yan Yatsunka Biyar Suke Gaban ldanuwanka, Haka Nima lna da Ilimin Duniya Kaf A Gabana.
-Labbaika Ya Kofar Ilimin Manzon Allah (S).
-Ni Dai Banga Abin Mamaki ga Wanda Manzon Allah (S) Yace: "Nine Birnin Ilimi Ali Shine Kofar Birnin".
-Muhammad Jiddah Nguru
07037009525