Wanda Yafi Kowa Tsananin Gaba da Shi'a Dansa Sai Yazama Shi'a!!!




—Sheikh Ibraheem Zakzaky [H].


“Tarihi abin da yake cewa; wanda yafi tsakanin gaba da shi’a ɗansa sai ya zama shi’a‚ kuma ya rasa yadda zaiyi da ɗan saidai ya kashe ɗan (Sedai in ze kashe ɗan ne)‚ se ya zama ɗan da yafi so‚ kuma se ya zama shi ya zama shi’a. Kunga Abin da ya faru da Yazidu ko? Se ɗan sa wani magajin sa mai suna: Mu’awuya sai ya zama shi’a su basu sani ba.”


“Se suka naɗa shi shine Sarki‚ bayan Yazidu. Ya kwana uku be fito fada ba‚ rannan ya fito yahau mimbari ya musu jawabi yace “Wannan mulki bana ubana bane ballan tana na gada‚ mulki na Ahalulbaiti ne‚ Saboda haka kuje kuyi mubaya’a ga Imamu Zainul Abidin” Se ya sauka.”


“Se suka ce ya’akayi ya zama shi’a ne? Waye ya koyar dashi Shi’i? Sai aka ce Malamin shi Malamin Allo ne (Malamin sa da yake koya masa Alƙur'ani)‚ aka ce Shine. Ashe Shi’i ne yana ɓoyewa. Se suje su yima Malamin yankan rago‚ yaron shima su yanka shi ina jin ko ɗan shekara 17 ne lokacin da suka yanka shi‚ shi ƙabarin sa yana nan ya wanzu, za kaji ana cewa wannan ƙabarin mu’awuya ɗan Yazidu ne‚ wanda ke ƙaunar Ahalulbaiti.”


@..17th-December-2022

©...Ibraheem Y. Ibraheem✍️

—Zakzaky Symbol of Peace

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post