Daga KUNDIN TARIHIN HARKA
Da yammacin ranar Juma’a 11 ga watan Disamba 2015 daidai da 29 ga watan Safar, 1437, shekaru bakwai ke nan da suka gabata wasu ‘yan iskan gari da aka yiwo hayarsu dauke da muggana makamai, suka sake aukawa ‘yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a karo na biyu a kasa da mako daya a kauyen Gabari dake karamar hukumar Zariya. Harin na wannan rana a wancan lokaci, ya yi sanadiyyar jikkata ‘yan’uwa 10, tare da kashe ‘yan’uwa 3.
Tunda safiyar wannan rana, wasu ‘yan uwa na yankin Zariya da kewaye suka je kauyen da nufin bai wa ‘yan uwansu kariya da ‘yan iskan garin suka aukawa a Juma’ar da ta gabata a wajen pre-khuduba a Masallacin Juma’ar garin. Sai dai tun isar su, sun tarar da ‘yan Iskan garin a kauyen dauke da muggan makamai, suna jiran lokacin sallar Juma’a ya yi su sake aukawa ‘yan uwan. A gefe guda kuma ga ‘yan Sanda motoci Hilux guda 3 da Babbar Mota guda 1 tare kuma da DPO na shiyyar Danmagaji Zariya.
Bayan kwashe tsawon Awanni ana kallon-kallo a tsakanin ‘yan iskan garin da ‘yan’uwan wanda suka je da niyyar kare kai daga harin da aka kai musu a makon da ya gabata, a karshe DPO ya yi alkawarin kama duk wanda yake da hannu wajen aukawa ‘yan’uwa a makon da ya gabata wanda ya yi sanadiyyar kashe dan uwa daya da kuma jikkata sama da 14.
Wasu ‘yan uwa da suka wakilcin sauran ‘yan’uwa suka je wajen ‘yan sandan aka yi abin da ake ce ma ‘SULHU’. Sannan aka roki ‘yan uwa suka fice daga garin ‘yan sanda na biye da su, amma sai aka bar ‘yan iskan garin a garin ba tare da DPO ko ‘yan sanda sun ce musu uffan ba.
Fitar ‘yan’uwa daga garin ke da wuya, ‘yan iskan garin nan suka zo da muggan makamai suka aukawa ‘yan’uwan da suka rage a garin da ba su gama fita ba. Wanda suka bar mutane da dama a kwance. Isar wannan labarin kunnuwan ‘yan’uwan da suka koma gidajensu ke da wuya, sai kalilan suka koma garin da nufin bayar da kariya.
Wani da aka jima mugun rauni ya shaida mana cewa; “a lokacin muna cikin garin, bamu san cewa ‘yan’uwa sun fita ba, sai muka yi niyyar dawo wa ta wajen Masallacin, a nan ne muka tarar da ‘yan iskan garin, ga shi mu kuma bamu wuce mu goma ba, da suka ganmu nan da nan suka hau mu da sara, da duka, muna karewa, suka jikata wasu a cikinmu, muka samu mu kuma muka kora su. Kuma lokacin da wannan ya faru, akwai Hakimin Tukur-Tukur a wajen, a gaban shi aka rufar mana da sara, amma bai hana su ba, bai kuma ce uffan ba,” Inji shi.
A lokacin da aka aukawa ‘yan’uwan da wannan yammacin, an tuntubi DPO na shiyyar Danmagaji domin shaida masa halin da ake ciki, sai ya ka da baki ya ce; “zai aika yaransa suka kawo karshen abin.” Sai dai bayan ya kashe wayarsa, an sake kiransa ba adadi, amma ya kashe wayar. Kuma har kura ta lafa ba a sake samunsa a waya ba. Kuma ba a ga wani Dan Sanda da ya je wajen ba. Bayanai a wancan lokacin sun tabbatar da cewa ba a iya dauko gawar wadanda aka kashe ba a wancan lokacin ba sai can cikin dare tukunna.
Su dai wadannan ‘yan taurin, an yiwo hayarsu ne daga Unguwar Hanwa, Tudun Wada duk a cikin garin Zariya. Wanda yake ‘yan Daba ne sosai na gaske. Adadin wadanda suka aukawa ‘yan uwan ya wuce mutane 300, kuma ‘yan uwa ‘yan kalilan ne. A binciken da majiyarmu ya yi a wancan lokacin, ya gano cewa; akwai sa hannun Masarautar Zazzau wanda kanin Sarkin Zazzau a wancan lokacin, Dr. Shehu Idris (Marigayi), wato Dan Isan Zazzau, Hakimin Tukur-Tukur, Alhaji Akilu Idris (Marigayi) ya wakilta. Kuma bincikenmu ya tabbatar da cewa; ga dukkan alamu akwai sa hannun DPO na shiyyar Danmgajin Zariya na wancan lokacin bisa yadda ya ki daukar kowanne irin mataki duk da korafin da aka kai masa.
Wakilin ‘yan’uwa na garin Malam Shafi’u ya tabbatar da sunayen wasu mutane wanda akwai sa hannunsu wajen aukawa ‘yan uwa a garin a yayin ganawa da majiyarmu a wancan lokacin, inda yake cewa; “lallai wadannan ‘yan tauri hayarsu aka yi, domin da can cece-kucen da ake yi ai da wadansu ne daga cikin garin, kuma bilhasali ma akwai masu sa su. Masu sa su babban su shi ne Muhammad Awwal, wanda shi ne tsohon wakilin ‘yan uwa, na biyu kuma akwai Hamisu, shi ne shugaban kwamitin Masallaci, sannan kuma akwai wani ana ce mishi Jibril, shima Memba ne na kwamitin Masallaci, sannan kuma akwai Bala Maiwada, shi kuma shi ne Sakatare. Da ni ne Sakataren Masallacin na shekara 16, sakamakon haka suka ce dole sai dai na ajiye musu Sakataren, sai na ce; ga shi. Wadannan hudun sune Ummul Haba’isu, sannan kuma akwai wani mai Unguwa na wurin, Alhaji Sulaiman, shima yana da hannu a ciki.” Inji shi.
Sakamakon wannan lamari da ya auku, masallacin an kulle shi ne, ba a yi sallar Juma’a ba a ciki.
SUNAYEN ‘YAN’UWAN DA AKA KASHE A WANNAN RANA
1. Shaheed Sulaiman
2. Shaheed Ali
3. Shaheed Zulyadaini
YANAYIN RAUNIN WADANDA AKA JIKKATA
Daga cikin wadanda aka sassara, wasu an sare su ne a wuya, wasu a ‘yan yatsu, wasu a hannu, wasu a kwauri, wasu a kafa. Wasu a Kai. Kuma mafi yawan wadanda aka sara, muggan rauni ne. wadanda rauninsu ya yi tsanani, tuni aka kai su asibitin Shika. A inda wasu kuma aka ajiye su a muhallin Husainiyya Bakiyyatullah, Zariya bangaren kiwon lafiya na Harkar Musulunci a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) wato ISMA ta yi musu aiki.
Kuma waki’ar Buhari ta ranar 12 ga watan Disambar 2015 (wacce za a tuna ta a gobe) ta rutsa da wasun su da aka ajiye a muhallin Husainiyyah Bakiyyatullah ana yi musu magani.