WAƘI'AR ZARIA: Shaheed Abdullahi Kudan A waƙi'ar Zaria 12 December 2015

 


Sunansa: Abdullahi, Sunan Mahaifinsa Musa Sunan Mahaifiyarsa: Rukayyat.

Shaheed Abdullahi Yana Ɗaya Daga Cikin Ƴan uwan Da Har Zuwa Ƴanzu Babu Labarinsu Da Haƙiƙanin Halin Da Suke Ciki, Sanadiyyar Harin Ta’addanci Da Sojoji Suka Kai A Husainiya, Zaria Da Gidan Shaikh Zakzaky (H) Dake Gyallesu Kan Ƴan uwa Almajiran Shaikh Zakzaky (H) A Ranakun 12, 13 Da 14 Ga Watan Disambar 2015. Ƙarkashin Jagorancin Hafsan Sojojin Nigeria Tukur Yusuf Buratai, Bisa Umarnin Gwamnatin Nigeria.


An Haifi Shahid Abdullahi Mai Kimani Shaikaru 18 A Garin Kudan Dake Jihar Kaduna Ta Nigeria. Ya Yi Karantunsa Na Primary A Garin Kudan A Makarantar "Yakubu Primary School Kudan". Sannan Ya Dora Da Karatun A Matakin Secondary A ‘Government Secondary School Kudan A Dai-dai Lokacin Da Yake Ƙokarin Ɗora Karatunsa Matakin Babban Secondary A Garin Katsina, Dai Kuma Allah (T) Ya Nufe Shi Da Samun Babbar Rabo Na Shahada.


A Ɓangaren Karatun Addini Kuma Ya Yi Karatun Zaure A Hannun Wani Malamin Zaure Mai Suna Malam Idris (Idi) Unguwar Tsauni Kudan. Baya Ga Haka Ya Yi Karatun Al'Qur’ani A Makarantar Nurul Huda Kofar Gidan Gardi, Ƙofar Arewa Kudan Daga Bisani Ya Juya Akalar Karatun Nasa Zuwa Makarantar Fudiyya Dake Garin Kudan.


MU’AMALARSA DA AL’UMMA

Shaheed Abdullahi Shahadarsa Ta Jikkata Zuciyoyin Al’umma Da Daman Gaske. Sakamakon Kyawawan Halayesa. Domin Kuwa Mahaifiyarsa Cewa Ta Yi “Tabbas Al’umma Da Dama Sun Tausaya. Bisa Wannan Rashi Na Shaheed Abdullahi. Kuma Hakika Ya Samu Kyawawan Yabo Da Zantuka Da Dama Daga Bakin Al’umma”,

Shi Shahid Abdullahi, Mutum Ne Da ALLAH (T) Ya Yi Masa Baiwar Hakuri Da Rashin Son Yin Magana Da Yawa. Domin Kuwa Koda Acikin Al’umma Ne Za Ka Samesa Ya Yi Shiru Ba Tare Da Yawaita Surutu Ba. Hakan Ya Sanya Ba Zaka Samesa Cikin Hayaniya Ko Wani Surutai Marasa Amfani Da Al’umma Ba.


Shahid Abdullahi Yana Daga Cikin Daliban Da Ba’a Taɓa Samunshi Da Abokin Fada Ba, A Cikin Ko A Wajen Makaranta. Tabbas Yawan Haƙurinsa, Ya Sanya Al’umma Da Daman Gaske Zubar Da Hawaye, A Lokacin Da Suka Sami Labarin Abida Ya Faru Dashi.

Ta Bangaren Yara Da Manya, Abokanai, Malamai, Iyaye Kowa Kalmomin Yabo Ke Fita Daga Bakinsu Akan Shahid Abdullahi. ALLAH (T) Ya Yi Masa Baiwa Iya Zamantakewa Da Jama’a Ta Kowace Fuska. Dalilin Da Ya Sa Ya Sami Shaidar Zama Mutumin Kirki A Idanun Jama’a


SHAIDU AKAN SHAHID ABDULLAHI DAGA BAKIN AL’UMMA

An Shaidi Shaheed Abdullahi Da Yawan Hakuri Don Kuwa Mahaifiyarsa Ta Furta Cewa: “Tabbas Shahid Abdullahi Mutum Ne Mai Yawan Hakuri Da Yawaita Uzuri Ga Al’umma Domin Wani Lokacin Mutum Ma Yakan Cutar Dashi Amma Maimakon Ya Dauki Matakin Ramuwa Sai Ya Zama Ya Dauki Matakin Juriya”.


Haka Dai Shahid Abdullahi An San Shi Da Yawan Kau-Da-Kai Ga Dukkan Abinda Bai Shafeshi Ba, Kai Ko Da Ma Abin Ya Shafeshi Yakan Kau Da Kansa Akai Matukar Ya San Ba Zai Zamo Maslaha Ga Al’umma Ba.

“Da Yawan Mutane Sun Faɗi Maganganu Masu Daɗi Akansa A Lokacin Da Suka Sami Labarin Abinda Ya Faru Da Shi Wasunsu Ma Da Yawa Ba Yan Harka Islamiyya Bane. Amma Sakamakon Kyawawan Dabi’unshi Ya Sanya Ya Sami Yabo. Sannan Kuma Da Addu’ar Fatan Alkhairin A Gareshi, Gami Da La’anta Ga Dukkanin Waɗanda Suka Zalunceshi” – Cewa Mahaifiyar Shahid Abdullahi.


Shaheed Abdullahi Ya Kasance Mutum Mai Matukar Baiwa Al’marin Iyayensa Muhimmanci Na Koƙarin Samar Da Farin Ciki A Zukatansu. Hakan Ya Sanya Ya Zama Jigo Ga Iyayensa. Ya Zamana Mai Kula Da Dukkanin Al’amarinsu. Domin Kuwa Ya Tsaya Kyam Wajen Neman Halas Dinsa Domin Ya Zama Ya Faranta Wa Iyayensa Da Dauke Dawainiyar Su.

DARUSSA A RAYUWAR SHAHID ABDULLAHI

Hakurinsa: Mun Riga Mun Yi Bayanin Wannan A Baya. Kuma Yan uwa Sun Fahimci Waye Shahid Abdullahi A Matakin Hakuri; Wanda Da Ace Kowa Zaiyi Koyi Da Shi Wajen Hakuri, To Da Lallai, ALLAH (T) Da Manzo Za Sunyi Alfahari Damu, Kuma Mu Sami Uzuri A Gobe Kiyama Wajen ALLAH (T).


Biyayya Ga Iyaye: Duk Da Karancin Shaikarun Shahid Abdullahi. Amma Lokacin Da Ya Yi Shahada Shi Ne Mai Kula Da Hidimar Mahaifansa Sakamakon Karfinsu Ya Kare. Duk Da Kuwa Yana Da Wasu Yan uwan. Amma Sai Ya Zama Yana Da Sana’ar Da Yake Yi Ta Dinki (Tailoring) Domin Daukar Dawainiyarsu Da Kula Da Farin Cikinsu. Kuma Haƙiƙa Ya Sami Yabo Ta Wannan Fannin Daga Bakin Mahaifiyarsa Da Sauran Al’umma.


Kyautarsa: Babu Wanda Zai Yi Wa Shahid Abdullahi Shaidar Cewa Shi Marowaci Ne. Domin Kuwa Sanin Kowane, Cewa Abin Hannunsa Baya Tsole Masa Ido Balle Ya Yi Rowa Akansa. Yawan kyautarsa Ce Ta Sanya Mutanen Gidansu, Musamman Yara Kanana Kullum Basu Da Wajan Miƙa Buƙatunsu Sai Gareshi. Don Kuwa Mahaifiyarsa Cewa Tayi “Lallai Wannan Bangaren (Kyauta) An Sami Yabo Daga Bakin Al’umma Kwarai Da Gaske.


SHAHADARSA

Shahid Abdullahi Ya Yi Shahada Ne Sanadin Baiwa Jagoransa Kariya Daga Mummunan Shirin Azzalumai Na Kashe Sayyid (H) Wannan Ne Yayi Sanadiyyar Rasa Rayuwarsa, A Yayin Da Suka Kai Harin Kisan Kiyashi A Husainiyya Da Gidan Shaikh Zakzaky (H) Dake Gyallesu A Ranakun 12, 13 Da 14 Ga Watan Disambar 2015 Wannan Ne Ya Rutsa Da Shahid Abdullahi Wanda Har Zuwa Yanzu Babu Tabbacin Halinda Yake Ciki.

Shahid Abdullahi Ɗan Kimanin Shaikaru 18 Da Haihuwa Kafin Rasa Shi, Ya Rasu Ya Bar Mahaifansa Da Ƴan uwansa.

Amincin Allah (T) Ya Ƙara Tabbata A Gareka Ya Shahid Abdullahi Ranar Da Aka Haifeka, Ranar Da Ka Yi Shahada Da Ranar Da Za Ka Tashi A Gaban Ubangijnka Kana Mazlumi Mai Arziki A Garesa.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post