KOTU TA HARAMTA SANYA HOTON SHAIKH ABDULJABBAR A KAFAR SADA ZUMUNTA.



Babbar kotun shari'ar Musulunci dake zaman ta a ƙofar kudu ƙarƙashin Mai Shari'a Alkali Ibrahim Sarki Yola ta yankewa Sheikh Abduljabbar Kabara hukuncin hukuncin kisa ta hanyar rataya dogaro da sashe na 392(b) na Kano state Shari'a Penal Code. 


Kotun ta yanke hukuncin ne bayan bayyana ra'ayin ta game da shari'ar da aka ɗauki tsawon shekara da watanni ana gudanarwa a babbar kotun shari'ar. Mai Shari'a Ibrahim Sarki Yola ya yanke hukuncin a yau Alhamis 15 ga watan Disamba, 2022 ya kuma yi umarnin a kwace masallatai biyu da malamin yake da su, Masallacin Ashabul Kahfi dake Gwale sani mai Nagge, da kuma Jami'urrasuli dake tukuntawa gidan maza a jihar Kano. 


Kotun ta kuma yi umarnin haramta wallafawa ko sanya hotunan sa da sunan yaɗa manufar sa, ta kuma haramta tallata aƙidar sa da sanya karatukan sa a gidajen Radio, talabijin da kuma kafafen sada zumunta, ta kuma yi umarnin ga gwamnatin jihar Kano da ta ɗauki ƴan sanda su kama duk wanda ya saba wannan umarnin. 


Amma a halin yanzu haka 60% na masu amfani da Facebook musulmai masu ƴancin tunani da hankali fes sun mayar da hoton Shaikh Abduljabbar Profile ɗin su. Duk inda ka gilma lungu da saƙon Facebook kyawawan hotunan Sarkin gida kake gani yana walwalawa. Wasu ma sun ce hoton Shaikh Abduljabbar ya zama DP ɗin su na dindindin.


Daga ƙarshe muna kira da kahafawa da su kwantar da hankalinsu su ci gaba da miƙa wa Allah Ta'ala al'amarin su, kada su manta da addu'ar Manzon Allah (SAWW) da yake cewa “La tahzan innallaha Ma'ana”, Insha'Allahu sun yanke abin da zai janyo musu baƙin jini ne.


Kuma albarkacin Annabin da ake yi domin shi, Malam Abduljabbar zai dawo cikin gida, kuma zai ci gaba daga inda ya tsaya har zuwa lokacin da Ubangijinshi ya ƙaddara mishi.


-Aba Sajjadi.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post