Sayyid Ƙasim ɗan Imam Musal Kazim (a.s.) ya lyi wafati a irin wannan rana ta 22 ga watan Jumadhal Ula cikin shekara ta192 daga hijirar Annabi a wata ruwayar , wanda aka binneshi a jihar Hilla (Babila) dake ƙasar Iraƙi .
TAƘAITACCEN TARIHINSA
Sunansa Al-ƙasim ɗa ne ga limami na bakwai daga jerin limaman shiriya watau Imam Musal Kazim (a.s.) kuma shine auta , an haifeshi a shekara ta 150 daga hijirar Annabi (saww) a birnin Madina mai tsarki , Imam musal Kazim ya kasance yana matuƙar kaunar Al-ƙasim har yana faɗa yana cewa a wata ruwaya :
Da ace Al'amari a hannuna yake (zaɓar Imami) da na sanya Alƙasim shine Imami a bayana saboda so da ƙaunar da nake masa sai dai lamarin a hannun Allah yake shine yake zaɓar inda zai sanyashi .
Lokacin da Daular Banul Abbas suka matsawa Sharifai Alawiyyawa da kisa da zalunci da danniya har takai ga Harunurrashid yana yanke hannun ƴa-ƴan Nana Faɗima (a.s.) da sauran nau'in uƙubobi ya tarwatsasu a duniya , daga cikin waɗanda suka gudu akwai Sayyid Al-ƙasim ɗan Imam Musal Kazim (a.s.) , ya gudu daga gida yabi gefen kogin furatu yana tafiya saboda yasan akwai kakansa Imam Ali (a s.) a wannan yankin (Najaf) , yana cikin tafiya a gefen kogin Furatu sai ya ga wasu yara mata su biyu suna wasan ƙasa ɗaya tana magana da ƴar uwarta tana cewa :
Ba haka bane na rantse da Ma'abocin bai'ar Ghadir (Imam Ali) ɗayar kuma tana bata haquri ,da yaji haka sai yace mata : wa kike nufi da wannan maganar ? Sai tace masa : mai suka da takobi biyu da mashi biyu Baban Hassan da Hussain , sai yace mata :
ya ke ƴata ko zaki kaini wajen mai wannan unguwar taku ? Sai tace masa : Ai shine Mahaifina , sai ta shiga gaba ya bita a baya har suka isa gidansu wajen mahaifin su kuma tayi masa iso , aka saukeshi a gidansu tsawon kwana uku kamar yadda yake a al'adar larabawa sukan kwanaki uku da baƙo kafin ma su tambayeshi daga ina yake ?
A safiyar kwana na huɗu Alƙasim yace da wannan dattijon (Mahaifin yarannan) : kasani naji daga wanda yaji daga Manzon Allah saww cewa :
baƙunta kwana uku ce abunda ya ƙaru akan kwana uku sadaka ne ni kuma banaso naci sadaka inaso ka samar min aiki a nan wanda zanyi na dogara da kaina .
Yayinda aka kwana biyu sai Dattijon nan yace da Alƙasim :
Wane aiki kake son kayi ? Sai yace masa ka sanyani mai shayar da ruwa a inda kake zama ?
Haka ƙasim ya cigaba da yi masa hidima har wata rana dattijon nan ya fito da daddare sai yaga Alƙasim yana ta Sallah da Ibadoji , daga nan sai soyayyar Alƙasim ta shiga ransa , washe gari ya tara danginsa yace musu : Inaso in aurawa Wannan bawan Allah na gari ɗaya daga cikin ƴaƴana , anan Alƙasim ya zauna har suka haihu da ita ya samu ƴa mace ya sa mata suna Faɗima .
WAFATINSA
Yayin da Alƙasim ya cika shekara 43 a Duniya sai rashin lafiya mai tsanani ta kamashi har ajalinsa ya kusanto , sai wannan Dattijo (sirikinsa) yazo kansa yana tambayarsa shin ko kana da Alaƙa da Banu Hashim ? Sai ƙasim yace : Eh ! Ni ɗa ne ga Imam Musal Kazim (a.s.) , take dattijon nan ya rikice yana kuka yana dukan fuskarsa yana cewa : me zancewa Mahaifinka Imam Kazim (a.s.) saboda abun kunyar danayi , sai ƙasim yace masa ba komai , anan Alƙasim yai masa wasiyya wacce take cike da mu'ujiza da sanya kuka da tausayi sannan ya cika ' Allahu Akbar .
An binne Alƙasim a wannan gari da ake kira (sur) wanda yanzu ake kiransa da Birnin Alƙasim cikin jihar Hilla ta kasar Iraƙi .
Yazo a wata ruwaya Imam Aliyur-ridha Yana cewa : Duk wanda bak samu damar ziyartata ba to ya ziyarci ɗan uwana Al-ƙasim .
Allah ka Sanyamu daga cikin masu ziyararsa ka bamu albarkarsa duniya da lahira .
✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey