Wacece Sayyadah Fadimah (as)



@Ma'asumah Nigerian News Updated

Itace Faɗima Az-zahra'u 'Yar Manzon Allah Muhammad ɗan Abdullahi ɗan Abdul Muɗallabi Nasabar su ta kai har kan Annabi  Isma'il  ɗan Ibrahim Mahaifiyar ta itace khadijatul Kubra Uwar Gidan Manzon Allah

Kuma ta taimaka Masa Da Dukiyarta, Lokacin Da Kowa Ya Hanashi.

An haifi Shugaba Faɗima a Makka ranar Juma'a (20) ga Watan Jumada Akhir Shekara ta Biyu Bayan aike.

Lokacin Da Sayyida Faɗima tazo Duniya ta zo ne tana Mai Sujjada Ga Allah kuma tana mai ɗaga yatsanta Zuwa sama Alamar kaɗaita Allah tazo Duniya tsarkakakkiya abar tsarkakewa.

Allah(t) Shi ne Ya Umarci Manzon Allah Da yasa mata Suna Faɗima, Ma'anar faɗima shi ne fansa daga Wuta

Sayyida Faɗima A's ta fara Ciwon ta Na ajali, Sakamakon Matseta da ƙyaure da Aka yi Alokacin Da Ake ƙoƙarin tilasta Musu Yin Bai'a ga halifa Abubakar

Aka karya Mata ƙashin haƙarƙarinta Aka Zubar Mata Da Cikinta Aka Kwace Mata Gonarta (Fadak) Aka Hanata Gadon Mahaifinta Aka keta Alfarmar Gidanta Aka juyar da halifancin Mijinta kuma Akaqi taimakonta😥😭

Sayyida Faɗima A's ta koma ga Allah ranar talata (3) ga jumada Awwal tana da Shekaru (18) da Wata 3 da kwana (15) a Duniya (Akwai Sa6ani).

Tabar Mijinta da 'ya'yanta, Hassan da Hussaini da Zynab da Ummu-kulthum.

Amincin Allah yaqara tabbata Agareki Masoyiya kuma Abar Alfaharina ranar Buruzinki da ranar Wafatinki da ranar da Zaki tashi ki tashemu💓

✍🏼Lamrat ta Sayyida Faɗima.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post