— Daga Jawabin Shaikh Zakzaky (H)
‘Who will bell the Cat’ wannan wata Karin magana ce ta yaren Turanci ‘Proverb’ da naji daga bakin su Sayyeed(H) a jawabin da suka gabatar a lokacin gabatar da walimar Karamar Sallah a muhallin Husainiyyah Baqiyyatullah Zaria, a shaikarar 2014. Su Sayyeed sun kawo wannan maganarce a lokacin da suke jawabi akan muhimmancin sadaukarwa ga Addini, da yadda al'umma ke bukatar wadanda zasu sadaukar domin tserartarwa daga bata. Shine a lokacin har su Sayyeed suka bada labarin yadda ya kasance tsakanin wasu Beraye 'Rats' da wata Kyanwa 'Cat'. Ga Mafhumin Labarin yadda ya kasance.
Akwai wasu taron Beraye, suna rayuwar su, saidai suna fuskantar matsalar wata Kyanwa, ya kasance takanyi musu dauki dai-dai, kullum takan lallabo ta cinye daya daga cikinsu, saiya zamana koda yaushe tana karar dasu, sai abin yayi matukar damunsu, sai suka hadu sukayi zama 'Meeting' a tsakaninsu domin nemawa kansu mafita daga sharrin wannan Kyanwa da take takurawa rayuwarsu. Daga karke suka yanke shawarar cewa, a samu bera daya daga cikinsu yaje inda wannan Kyanwa take domin ya daura mata Karaurawa 'Bell' ta yadda duk lokacin da tazo cinye su, to zasu ji karar wannan karaurawar sabida dole karaurawar zatayi kara, ta hakane zasu san da zuwanta, domin su tseratar da rayuwarsu. Saidai ba anan gizo ke sakarba, akwai sharadin duk wanda yaje domin dauarawa wannan Kyanwa Karaurawa to lallai zai rasa rayuwarsa, domin wannan Kyanwa zata cinyesa. Saidai kuma zai kasance ya fanshi rayuwar 'yan uwansa da tasa rayuwar. Amma daga karke sai aka rasa wanda zai sadaukar da rayuwarsa a cikin wadannan Beraye domin yaje ya daurawa wannan Kyanwa Karaurawa don ceton rayuwar 'yan uwansa. A sanadiyyar rashin samun wanda zai sadaukar da rayuwarsa, hakan ya sanya wannan Kyanwa taci gaba da lallabowa tana cinyesu daya-bayan-daya har ta gama dasu. Wannan shine asali da ma'anar kalmar 'Who will bell the Cat' ma'ana, wa zai daurawa Kyanwa Karaurawa.
A karshe sai su Sayyeed suke cewa, To kaga Illar rashin sadaukarwa kenan, da ace an samu daya daga cikin wadannan Beraye ya sadaukar da rayuwarsa, to da ya ceci rayuwar sauran, amma rashin samun wanda zai sadaukar din, saiya janyo rasa rayuwar tasu baki daya.
Koda su Sayyeed su zo karshen wannan labari, sai nace Allah Sarki. Su Sayyeed Kenan masu Ilimi da aiki. Wallahi babu abinda zuciyata ta sauwara min dangane da wannan labari, Illa saudaukarwar su Sayyeed domin ceton rayuwar al'umma. Kalli yadda su Sayyeed su sadaukar da lokaci, dukiya, Iyali, da dukkanin wani abu mai daraja a garesu, hatta rayuwarsu baki daya, ba domin komi ba, illa sai domin tsamar da al'umma daga bata, da sama musu uzuri a wajen Ubangiji a ranar Lahira.
Ya Allah Ka dubi wannan sadaukarwa ta Sayyeed, Ka girmama ladan wannan aiki nasu, Ka saka masa da mafi kyawun sakamako na Alkhairih, tun anan Duniya har zuwa Lahira. Ya Allah Ka kubutar da shi daga dukkanin tarkon Makiya, na sarari dana boye, tare da dukkanin Masoyansa baki daya. Alfarmar Sayyada Zahra da Abbanta da Mijinta da 'Ya'yanta ma'abota tsarki(A.S). ILAHEEY AJIB YA RABB.
— Abbakar Ibraheem Kudan.