Usulud-din(Asalin Addini)

[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


 [FIQHU]

USULID-DIN(ASALIN ADDINI).

Na Uku

Part Three 3.


Taskar.

®Hamidiyyun Press


SIFFOFIN ALLAH MADAUKAKI

Allah (SWT) yana da siffofi masu yawan gaske cikinsu akwai:


DAUWAMAMME: Allah ta'ala jimamme ne ya kasance kamin ko wanne abu sannan ya halicci abubuwa, haka nan shi kadai zai rage bayan rashin dukkanin abu har abada, haka allah mabuwayi gagara badau ya fada cikin littafinsa: kuma mu ne muke kaddara mutuwa a tsakankaninku sannan ba muzama masu gajiyawaba.

Imam abu hassan ali ibn musa ar-ridah (AS) Yace: allah tabaraka wa ta'ala jimamme ne, kuma jumawa itace siffa a gareshi,wanda ta yi nuni ga hankali cewa lalle babu wani abu gabanin sa, haka ma babu abin d zai kasance tare da shi wajen dawwama.


MAI MAGANA: Shi allah ta'ala yana magana da wanda yaso cikin annabawa da bayinsa salihai da mala'ikun sa, kamar yadda ya fadi haka cikin alkur'ani mai girma: kuma allah ya yi magana da musa magana sosai.

Hadisi daga imam amirul muminina ali ibn abi talib (AS) Yace: mai magana ba tare da ganinsaba.


GASKIYA: Allah ta'ala ya kasance mai gaskiya sabida yana daga cikin sifofinsa wato as-siduku, duk wani adan da yake fadi to ba ya sabawa, haka ma kuma baya saba alkawarinsa. kamar yadda shi allah ma'abocin hikima ya fadi haka cikin littafinsa mai tsarki: kuma wane ne mafi gaskiya daga allah ga labari?



Imam ja'afar As-sadik (AS) Yace: lalle mabuwayi mai tilastawa ya saukar maku da littafinsa, shi mai gaskiya ne mai ginawa hakama yana daga cikin siffofinsa kebabbu, cewa shi allah ta'ala mai halitta ne, mai azurtawane, mai rayawa da kaahewa ne, mai bayarwa da hanawa, haka ma kuma mai jinkai ne, mai gafartawa mavuwayi, mai daraja da karamci.


Ku sauraremu a fita ta hudu


Hamidiyyun Press

18 Dec,2022

08138011553 For WhatsApp group

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post