A ƙasar Somalia, saurayi yana aure ne tsakanin shekara 17 - 18. In ya kai shekara 20 ba tare da ya yi aure ba toh a wannan lokacin dattijan ƙabilarsu zasu saka baki akansa domin zai jawo musu abin kunya da zagi a wajen sauran ƙabilu.
Saurayi a Somalia yana da ƴancin zaɓar matar farko ba tare da wani yace masa uffan ba.
Idan Matarsa ta yi haihuwar farko, toh Mahaifiyarsa zata zaɓa masa mata ta biyu.
A irin Al'ada ta ƙasar Somalia, mutum zaiyi murnar cikarsa shekara 30 ne da auren Mata ta 3.
Wajibi ne ya auri Mata ta 4 kafin ya kai shekara 40. Suna ganin ƙurewar abin kunya ne mutum ya kai shekara 40 bai auri Mata 4 ba.