TARIHIN ABBAKAR IBRAHEEM KUDAN
GABATARWA:
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jinƙai. Tsira da Amincin Allah su Tabbata ga Fiyayyen Halittu, Annabin Rahama ( S ) da iyalan gidansa Tsarkaka.
Tarihin Abbakar Ibraheema, Asalinsa da kuma tsatsansa asalin mahaifin Abbakar, sunan Mahaifinsa Ibraheem. dan cikin garin Kudan, “ Gidan Gadi”, anan akahaifi mahaifinsa. Sunan mahaifiyar sa, A'isha an haifeta a gidan malamai acikin garin Kudan.
HAIHUWARSA.
An haifi Abbakar Ibraheema acikin garin Kudan, ashekarar 1996, a watan 19th April. Acikin garin Kudan ya ta so inda ya fara karatu a makarantar Yakubu l.g.a ( Primary School ) dake garin kudan ya kasance ɗalibi mai ƙwazo wanda ya samu nasara acikin matakin farko na fara karatunsa lokacin yana ɗan primary school. Aji 3 uku matsayin gwarzo Ashekarar 2004.
MATAKAN DA YA TAKA:
Abbakar: Ya taka wani matsayi wanda babu wani ɗilibi da ya takasa ashekara 2008, aloƙacin yana ɗan aji 2 acikin Fudiyya dake garin kudan, ya sa mu karramawa daga gwarazan malaman wannan makaranta ta Fudiyya, suka karramashi a matsayin ɗalibi da yazo mataki na ɗaya a jarabawar ( 1st Position ); ya zamto gwarzo wanda ya zama zakara acikin sauran ɗaliban dake cikin wannan makaranta.
Haka Zalika Abbakar yana ɗaya daga cikin 'yan Faretin dake cikin Fudiyya kudan wanda ya zamto yana jagaba wajan taka Fareti, ya samu kyautar wukilci ta yan Fudiyya daga Hannun “( Sayyid Ibraheem Zakzaky Hafizahullah); a shekarar 20010, ya amshi kyauta ne daga hannun Jagoran Harkar Musulimci dake Najeriya. Cikin birnin Zaria dake Jahar Kaduna. Daga hannu mai Albarka na Shaikh Ibraheem Zakzaky, loƙacin da suka wukilci Fudiyyah kudan a gasar “ kacici-kacici ( Quiz ) inda ya sa mu tagomashi daga hannu mai Albarka ya karɓi kyautar ahannun Sayyid Ibraheem Zakzaky Hafizahullah. Samun nasara da Kudan ta yi na zuwa na biyu ( 2nd position).
KARATUNSA DA KUMA NASARAR DA YA SAMU A ƘARAR GHANA.
Abbakar: ya samu nasara daga cikin nasarori, nasamunyi karatu a ƙasar ( Ghana ); ashekarar 2016 Allah ya nufeshi da zuwa karatu ƙasar Ghana makarantar “ Imam Ja'afar Teacher Training Centre Kumasi-Ghana”. Inda ya samu nasara ta karramawa daga malaman dake cikin Makarantar Imam Ja'afar dake ƙasar Ghana. Ya sa mu wannan karmawar ne ya yin da yake matakin ƙarshe na kammala jarabawar ƙarshen Shekara da matsayin 'Mumtaz' ( Excellent ).
KARRAMAWAR DA YA SAMU DAGA SHAIKH MUHAMMAD TURI.
Abbakar Ibraheem: a shekarar 2019, ya samu nasara na zamowa ɗaya daga cikin marubutan da suka taka rawa sosai wajan binkice akan abin da ya shafi tarihin Rayuwar Shaikh Turi, ya kasan ce yana halartar dukkan wannan gasar Duniya ta marubuta da akeyi a birnin kano, dukkan shekara yanzu kusan Shakara 5 zuwa 6 ne da fara shiga wannan gasar da akeyi a ƙofar w/ka, dake birnin Kano.
Tunda ya fara wannan gasa bai taɓa zuwa ragoba sai dai sunansa ya fito daga cikin za ƙakuran gasar da akasa, Shaikh Turi ya karrama Abbakar kusan ta shi 6 ke nan da fara wannan gasa ta duniya. Kwamitin shirye-shiryen munasabar Shaikh Turi suna yawan jin-jinawa Abbakar akan yadda dukkan shekara sai ya samu nasara zuwa cikin zakarun gasar.
2020: Ya ƙara samun Girmamawa tare da ba da kyauta ta Musamman daga Shaikh Turi, inda ya ke samun sheda sosan gaske daga malaman da suke bashi kyauta, daga cikin malaman da suke bashi kyauta akwai Malam Aliyu Rimin Gado. 2020, 2021, 2022, dukkan su ya samu nasara a gasar Duniya ta Shaikh Turi.
KARRAMAWAR DA MAKARANTAR MA'AHAD RASULIL-AKHRAM KUDAN TA YI MASA.
A 2022, makaranta Ma'ahad Rasulil-Akram Kudan, ta karramashi da kyauta ta Musamman, yadda ta shedai shi da jajircewar sosai akan abin da ya shafi koyarwa da wasu abubuwa na kula da ita Makarantar.
ZAMAN SHI MA'KACIN JARIDAR MA'ASUMAH RADIYO.
ATAƘAICE:. Ya na ɗaya daga cikin marubuta dake kula da shafin Ma'asumah Nigeriya News update, ya na ɗaya daga cikin ( Editer ) wanda yake kula da dukkan wani abu dake wannan Jaridar, Haka zalika kuma ya kasance ɗaya daga cikin C .I. O na “ Radiyo ” Ma'asumah radiyo online. Shine wanda ya ke jagorantar wasu abubuwa masu yawan gaske.
MU'AMULLARSA DA MUTANE.
Abbakar: yana da mu'amulla Da kyau Ta-ta zato ga al'umma sosai ya samu yabo daga Al'umma sosai hatta har da mutane dake zaune a ƙasar Ghana wanda ba su so tafiyarsa ba. Amma lokaci ya yi haka kuma ya samu sheda wanda ya zamu mutum wanda yake da zuminci da ziyartar 'yan uwansa na dangi da sauran al'umma, haka zalika Abbakar ya kasance wanda abin duniya bai rufe masa ido ba.
Wannan shine tarihin Rayuwar Abbakar Ibraheema Kudan a taƙaice.
Daga: Faruq Sani ( Abban Jeedderh ) tare da Aliyu Nuradeen