Taron wanda aka yi shi har kashi biyu, kashi na farko shi ne, Excursion wanda aka yi da safe misalin ƙarfe 9:00 na safe zuwa 12:00 na rana, sai kuma a daren ranar da aka gudanar ainihin program ɗin.
Taron ya gudana ne a muhallin Fudiyya Minna, Niger State. Taron wanda ya samu halartar baƙi daga wuraren daban-daban, haka kuma taron ya fara ne da misalin ƙarfe 8:00pm har zuwa 11:00pm na dare.
Malama Narjis Usman ne ta fara buɗe taro da addu'a, sai karatun Alƙur'ani mai girma daga bakin Narjis A. Umar, sannan sai ziyarar Sayyida Zainab (SA) daga bakin Ummul-Khursum Anas, daga nan kuma ƴan INTIZAR da ƴan JAISH suka gudanar da display, sai kuma masu taron (ZAINABIYYUN) suka gabatar da quiz, daga nan aka karanta paper presentation daga bakin Mal. Zahra'u Ibrahim Khalil.
Malama Nusaiba A. Umar ta gabatar da mai jawabi wato Malama Kausar Ibrahim, inda Malamar ta taɓo ɓangarori daban-daban Musamman abin da ya shafi Muhimmacin shi kansa Ilimin, daga ƙarshe kuma sai aka yanka Cake wanda Malama mai jawabi ta gabatar, sai jawabin godiya daga bakin Nusaiba Musa daga nan kuma aka rufe taron da addu'a.
Rahoto Daga: JASAZ Media Maitham At-Tammar Zone.
Tags:
Labaran Duniya