@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@
... Umar Hassan Gololo...
Shugaban kasa Musulmi, Shugaban rundunar Sojoji Musulmi, Shugaban ''Yansanda Musulmi, Shugaban Hukumar tsaro na DSS Musulmi, Ministan tsaro Musulmi, National Security Adviser Musulmi amma a haka Sojojin Nigeria suka dirarwa Musulmai da kisan gilla, kisan mugunta da rashin tunani ballantana hangen nesa ko tausayi, suka yi kisan gillar da ba a taba yin irinsa a tarihin Arewa ko Nigeria ba.
Kisan da aka yiwa Maza da Mata, Yara da Manya ta hanyar amfani da bindiga, konawa da wuta da takawa da tankar Yaki.
Abin mamaki da al'ajabi Malaman da suka goyi bayan zaluncin da aka yi duk Musulmai ne, wadanda suka yi wakokin yabon ta'addancin Gwamnatin Buhari akan Malam Zakzaky(H) Musulmai ne, wadanda suka rinka murna, walima da caje aljifan gawarwaki suna satar kudade da yanke yatsu suna cire zobe Musulmai ne.
Wadanda suka rinka zanga-zangar kira ga Gwamnatin Buhari kada ta saki Malam Zakzaky(H) da kuma cigaba da kashe Almajiransa Musulmai ne.
Menene zai baka mamaki idan aka ce wadanda suka bada umurnin a kai hari Gidan Sayyida Fatima Alaihassalam Musulmai ne?
Menene zai baka mamaki idan aka ce wadanda suka kai hari Gidan Sayyida Fatima Alaihassalam Musulmai ne?
Menene zai baka mamaki idan aka ce wadanda suka daki Sayyida Fatima Alaihassalam suka cinna wuta a Gidanta Musulmai ne?
Shin laifin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa Alihi ga makiyansa ne ya shafi Sayyida Fatima Alaihassalam ko kuma tsananin kiyayya ne a gareta kawai?
Kana tsammanin wanda yake son Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa Alihi so na hakika zai kai hari Gidan Sayyida Fatima Alaihassalam?
Me yasa ake tsinewa Munafukan da suka cutar da Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa Alihi a boye amma ake yabo da jinjinawa wadanda suka daki Sayyida Fatima Alaihassalam?