[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Ita yarinyar 'yar ƙasar Morocco ce, mai shekaru 9 na haihuwa, ita ce wacce kwanaki su Ghali Ibrahim da sauran fans ɗin da ba sa ƙaunar Ronaldo suka yi ta saka biyon yadda ta riƙa yi wa masa kalamai na rashin girmama nagartarsa a ƙwallo tana dariya a lokacin da shi yake kuka silar cire ƙasarsa daga gasar cin kofin duniya da Morocco ta yi, wanda hakan ya kawo ƙarshen mafarkinsa na cin kofin duniya saboda wannan ne karo na ƙarshe da za a sake ganinsa a kofin. Babu ko shakka abin da ta yi a lokacin bai yi wa magoya bayan Ronaldo daɗi ba (ciki har da ni) ta yadda da dama sun so ƙasar (Morocco) ta lashe kofin duniya, amma tun bayan abin da ta yi, sai ya zamana kusan duka fans ɗin Ronaldo sun juya baya tare da fatar a cire su.
Aikuwa bayan an cire su ɗin, fans ɗin Ronaldo sun yi ta video iri-iri suna mayar mata da bikin da ta gayyata. An ce hakan kuma ya taɓa yanayin lafiyar yarinyar ta, don na saurari muryar wata dattijuwa (da ta ce mahaifiyarta ce) tana bayar da haƙuri ga Ronaldo da magoya bayansa, in da ta bayyana ɗiyar tata ba ta yi daidai ba; amma a yi mata uzurin yarinta saboda shekararta 9 kacal. Ta bayyana yarinyar ma ba ta kallon ball, kaɗai ta ɗauka ta wannan hanyar ne za ta bayyana farincikinta ga nasarar da ƙasarta ta samu a kan Ronaldo. A cewar matar, a yanzu da videos suka yawaita na mayar wa yarinyar bikin da ta taro, hakan ya taɓa zuciyarta, har ta kai ba ta cin abinci, walwala ta ƙaurace mata, ta daina wasanni da 'yan uwanta, an ce ba ma ta gane abubuwa da dama....a taƙaice dai, depression ya ƙulla ƙawance da ita.
Daga cikin maganganun da yarinyar ta faɗa akwai in da ta ce, "Where is Ronaldo? He's crying in his car! Portugal, airport that way." Ta yi maganar ne tana dariya bayan ta yi alamar zagi da hannunta. A yanzu kuma da lafiyarta ke cikin halin ni 'ya su, a ƙarƙashin videon da mahaifiyar tata ta bayar da labarin halin da yarinyar ke ciki magoya bayan Ronaldo suna ta comment amma duk ciki uku sun fi jan hakalina kamar waɗanda suka ce, "Anyway, mental hospital that way." (An rubuta irin wannan comments ɗin da yawa). Sai kuma biyu da suka fi jan hankalin mutane wanda an yi likes aƙalla kusan 800 a comment ɗin da ya ce, "She is just a kid is what everyone saying, if she is old enough to know how to make fun of Ronaldo then she is old enough to know not to disrespect people especially older than her." Comments na uku da ya fi jan hankali shi ne wanda ya ce, "Ronaldo has children from about a year old to 10 or 11 maybe 12. His kids will also go through same because even kids are making fun of their dad, that's even extremely depressing. Next time raise your kids well. Trolls are for those who handle it's consequences."
A ganina, tun farko ya dace a nusar da yarinyar abubuwan da ta yi ba daidai ba ne kamar yadda masu comments suka bayyana, don a hankalce kuskure ne kukan wani ya zamto abin aibatawa balle wanda ke da ɗan da ya girme ta. Ko ba don wannan ba, ya dace a nusar da ita lallai reshe ka iya juyewa da mujiya (a cire su) a yi mata abin da ta yi, musamman duba da ta taɓo wanda a iya istagiram yana da magoya baya miliyan ɗari biyar da ashirin da ɗoriya, ban da na sauran kafafe irinsu twitter, facebook da saura.
Babu shakka na tausaya mata, na tausaya wa mahaifiyarta, sai dai ban yi mamaki ba. Domin dai na san da ma za a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. Allah ya ba ta lafiya, amin.
Muttaka A. Hassan
(Abu Ahmad)