SUN YI IYAKAN KOKARINSU SU BAKANTA SIFFARMU A IDON DUNIYA, AMMA SUN MAKARA




__Sheikh Ibrahim Zakzaky (H)


"Sun yi iyakan kokarinsu su bakanta Siffarmu a idon duniya Amma sun makara, saboda muna tare da mutane ne. Mun fi su kusa da mutane. Su mahukunta da yawa nesa suke da mutane, mu kuwa kusa muke  da su. Kuma kar a manta, abin da yake zukatan su (Suke Hankoro) shi muke fada, ba wani bako muka zo musu da shi ba. 


An yi iyakan kokari a shafa mana mummunan fenti amma ya faskara. To amma dai basu fidda rai ba. Shiyasa kuma wannan karon suka yi hankoron wanda za su yi na karshe. wato za a yi ta manya manya ta kare, a yi a gama. kamar yadda suka kira shi "Once and for All". A yi ta manya manya ta qare, daga yanzu baza a sake kiran komawa addini ba, aji tsit. Sai dai kuma ma in za a yj addini sai irin yadda suke buqata. irin kungiyoyin da suka kirkiro, suke kafirta musulmi, suke sabbaba fada tsakanin musulmi da musulmi, kuma suke ingiza musulmi su yi fada da kirista. kabila suyi fada da kabila, da bangare suyi fada da bangare. Duk su suke ingiza Wannan


SHEIKH ZAKZAKY (H) YAYIN ZIYARAR 'YAN UWA NA KANO.  20/11/2021


19/12/2022

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post