Sirrin As'habul kisa'i

 


@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@


A cikin shekara ta 1951, wata kungiyar kwararru masu bincike a kasar Rasha, su na bincike a cikin ruwan dutsen Ka'at (Judi), sai suka gano wasu guntayen katakwaye, da su ka ci gaba da haka sai suka ga wani babban katako, saboda kwakkwafin su sai suka fahimci akwai saura, su ka ci gaba da tuno har suka samu wani mai fasalin (Triangle), mai kimanin 14" × 10", wannnan shi ya fi sauran adanuwa. A jikin wannan katakon sai suka ga wani rubutu na wani dadadden yare, wannan ya su yin kwakkwafin gano wani abu akan katakon. Bayan bincike mai yawa a shekarar 1952 suka tabbatar da cewa wannan katakon na jirgin Annabi Nuhu (AS) ne.


Bayan sun tabbatar da haka sai suka shiga bin kwakkwafin gano ma'anar wannan yaren da ya ke rubuce a jikin katakon.Gwamnatin wannan lokaci ta kafa kwamitin kwararru ma su bincike na mutum 7 a bangaren sashin binciken su. Wannan kwamiti ya fara aiki 27th February, 1953, bayan wata 8 masu binciken su ka tabbatar da wadannan guntayen katakwayen duk na jirgin Annabi Nuhu (AS) ne, kuma wannan mai fasalin (Triangle) da rubutu a jikinsa na jikin jirgin don kariyar jirgin ruwan ne da kuma neman alfarmar Ubangiji (SWT).


Abin mamaki, akwai wani zane a jikin wannan katakon daga tsakiya, shi kuma yaren harshen 'Saamaani' ne.


Wani kwararre akan dadaddun yarirrika da Manchester, kasar England wato Mr. N.F Max, ya fassara wadannan kalmomi dake jikin katakon da harshen turanci, ga yadda fassarar take da hausa: Ya Ubangijina, mataimaki na, ka ajiye hannuna da jinkai, don girman tsarkakan jikkunan: Muhammad, Alia (Ali), Shabbar (Hassan), Shabbir (Hussain) da Fadima.


Dukkan su masu girma ne kuma madaukaka. An hallici duniya ne domin su, ka taimaka ni don sunayen su.


- Muhammad Ahmad

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post