A gobe Asabar shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai cika shekara 80 da haihuwa.
An haifi shugaba Buhari ne a ranar 17 ga watan Disamba a garin Daura da ke Katsina.
Tuni manyan mutane da 'yan siyasa suka soma tura sakon taya murna ga shugaban kasar.
Cikin wadanda suka soma aike sakon murnarsu ga shugaban akwai dan takarar shugabanci kasa a inuwar Jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da kuma shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila
Tags:
Labaran Duniya