Kamar Yadda Jiya Muka Kawo Makamancin Wannan Daga Shehu Ibrahim Inyass (R)
Acikin Littafin "Hisunul Afhami Min Juyushil Auhãmi"
Shehu Usmanu Danfodiyo (R) Yace: Yana Daga Cikin Abinda Yake Kuskure Ne Cewa Sashen Mutane Waɗanda HASSADA Ta Rufe Musu Idanu Suna Cewa: Abinda Yake Dai-dai Shine Barin Shagaltuwa Daga Yin Tãlifai (rubuce-rubuce na ilimi) Da Ake Wallafawa A Yau, Domin Tãlifan Magabata Shuwagabanni Mafiya Sani Sun Gabata, Basu Bar Komi Ba Gare Mu Wanda Muke Buƙatuwa Gare Shi Komi Sun Rubuta Sun Bar Mana, Kuma Sune Mafiya Cikakken Ilimi Daga Masu Yin Tãlifi A Yau,
Sai Shehu Ɗan Fodiyo Yace: Wannan Maganar Itama Ɓa Tattacciya Ce Bisa Ijma'i Domin Kowane Mallami Yana Kiyaye Wa Ne Acikin Tãlifin Shi (Rubutun shi) Abinda Al'ummar Zamanin Shi Tafi Himmantuwa Dashi, Tafi Buƙatuwa Gareshi, Domin Shine Mafi Sani Da Wannan, Sabida Haka Sai Tãlifin Kowane Mallami A Zamanin Shi Ya Zamo Shine Mafi Amfanarwa Ga Mutanen Wannan Zamanin Daga Tãlifin Wanin Shi.
Shehu Ɗan Fodiyo (R) Yace: Yana Daga Abinda Yake Kuskure Ne Shine Cewa Sashen Mutane Suna Ganin Ya Nisanta Ace Allah Yayi Buɗi Ga Wani Daga Cikin Waɗanda Suka Zo Daga Baya Da Abinda Bayyi Buɗi Da Shi Ba Ga Waɗanda Suka Gabata Na Shehunan Su A Babin Ilimi, Wannan Shima Magana Ce Ɓatacciya Kuma Wahami Ne Bisa Ga Ijma'i.
Domin Falalar Allah Ta Kasance Bata Taƙaituwa Da Zamanona Da Wurare, Shi Allah Mai Iko Ne Akan Komai, Ta Yaya Zasu Nesanta Wannan Alhali Allah Ta'ala Yana Cewa: Ka Gaya Musu Ya Muhammad! Lallai Falala Tana Ga Allah Yana Bayar Da Ita Ga wanda Ya So., Kuma Allah Yace: Allah Yana Zaɓar Wanda Ya So Da Rahamar Shi, Allah Ma'abuci Falala Ne Mai Girma.
Akwai Cigaba....... !!!
Wannan Kukan Kurciya Ne Ga Masu Cewa Sheikh Dr. Abduljabbar Kabara (H) Kowa Bai Gane Waɗannan Abubuwan Ba Se Kai? Suna Kuma Kushe Tãlifan Da Yayi Da Kuma Waɗanda Yake Kan Yi A Yanzu Da Hujjar Irin Waɗannan Mutanen Da Shehu Yake Magana Akan Su.