[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Umar Hassan Gololo ✍🏼
Na ga mutane dabam-dabam, daga yankuna dabam-dabam, addinai dabam-dabam da fahimtu dabam-dabam suna kai wa Malam Zakzaky(H) ziyara a Gidansa dake Abuja, duk da kuwa Gwamnatin Buhari ba ta son sa.
Shin Malam Zakzaky(H) yana raba Kudade, Gidaje da Motoci ga wadanda suka ziyarce shi ne?
Idan Malam Zakzaky(H) kudade, Gidaje da Motoci yake rabawa Sanatan nan na Kudancin Kaduna, Hamza Almustafa da su Deji Adeyanju da Sowore da Kungiyar Igbo Community zasu je kuwa?
Amsa ba zasu je ba, saboda me? Saboda Malam Zakzaky(H) ba shi da kudade, Gidaje da Motocin da zai ba su.
Shin Kudade, Gidaje da Motoci sune kadai burin rayuwar Dan-Adam?
Amsa ita ce a'a.
Malam Zakzaky(H) yana da abubuwan da ya mallaka wadanda sun fi kudade, Gidaje da Motoci.
Menene wannan abun?
Amsa ita ce sakon Allahu Ta'ala irin wanda Annabawa da Manzanni Alaihimussalam suka zo da shi.
Sannan Malam Zakzaky(H) yana da gaskiya ita kuma yake fada musu, domin kuwa wallahi Summa Tallahi da makiyinsa da masoyinsa babu wanda ya isa yace ya taba yi masa karya.
Duk kuwa wanda zai fada maka gaskiyar daga ina ka fito, me ka zo yi kuma ina zaka shi ya kamata ka rike hannu bibbiyu.
Muna rokon Allahu Ta'ala Ya fahimtar da al'ummar Nigeria manufar Malam Zakzaky(H) da da'awarsa Alfarmar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa Alihi wa sallam.