Shin Likita Ko Macce Me ciki [ Juna Biyu ] tana Iya yin Al'ada , Kamar Yanda Ta Saba na Wata-Wata ??




Daga: Arrida Chemist💊Shinkafi


🕌BARKA DA JUMA'A🕌


A'a hakan baze yiyuba idan macce me

ciki tafara ganin jini to wannan alamun

matsalane wanda cikin ma yana iya zubewa wato (miscarriag)


A gaskiya idan Macce tana dauke da juna 2

tabbas bazata taba yin al' ada ba saboda al'ada tana zuwane kawai ga macce wadda

batada Ciki. duk bayan wata 1/ kokuma kwana 28


TABBAS IDAN MACCE ME CIKI TANA GANIN JINI LOKACIN DA TAKE DA CIKI

WATA 2/ KO 3 HAR ZUWA 4 TO GASKIYA AKWAI MATSALA


Saboda macce me CIKI batayin al' ada hasalima idan macce me ciki tafara ganin alamun zubar jini a jikin ta (al'aura) to tayi gaggawar daukan mataki saboda ba al' ada bace, alamun zuwan wata matsalace



TO LIKITA MIKESA ZUBAR JININ BA LOKACIN

AL' ADA BA


Matsalolin dake kawo jubar jini ga macce


1. miscarriage alamomin yin bari ko zubewar ciki


2.ectopic pregnancy( ciki bayan mahaifa )


3.placenter problems 


4.infection of the placenter(kwayoyin cuta cikin mahaifa)


5.molar pregnancy (kamar ciki. karya)


SHAWARA GA ME CIKI IDAN TANA GANIN JINI

YANA ZUBAR MATA


1. Gaggawar zuwa ganin likita domin baki kulawa wadda tadace

Saboda ayimaki photo agani idan cikin

rabinsa ya zube kokuma da

sauransa


2. A Gujema da tsayawa gida ayi treatment

Saboda tsaya gida babban hadarine Saboda idan juna biyu rabinsa ya zube aka bar sauranshi bai zubeba duka, sai  kikasha maganin tsaida zubar jinin to ze iya

haifar maki da cuta kokuma.toshewar mahaifa kokuma molar gestation Wanda akecema kwanci


ABUBUWAN DAKE YAWAN SA BARI

(MISCARRIAGE)


1.yawan shan Abu me daci sosai


2.yawan saduwa lokacin da ciki yake dan

karami


3.yawan aikin wahala da dauka. Abu

me nauyi


4.yawan shan maganin Hausa barkatai


5.yawan shan magani na kwaya bada izinin

likitaba


6.infection (kwayoyin cuta su shiga mahaifa)

da sauransu


ALLAH YASA MUDACE

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post