Ga Kadan Daga Cikin Laifuffukan:
Daga BARR. Hashim Hussein Hashim Fagge
.
1. Wai a Hadisi aka rawaito, Mahaifiyar Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam Aminatu bint Wahab 'yar wutar jahannama ce, sai Mallam Abduljabbar ya ce wannan karya ne, tatsuniya ce.
2. Wai a Hadisi aka rawaito Mahaifin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam Abdullahi bin Abdulmudallab Dan wutar jahannama ne, sai Mallam Abduljabbar ya ce wannan karya ne kuma tatsuniya ce.
3. Wai a Hadisi aka rawaito Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ya na fitsari a tsaye akan bola, har wani ya zo wucewa zai juya sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce masa ya tawo ba komai. Sai Mallam Abduljabbar ya ce wannan labarin kanzon kurege ne, karya ne , ba'a yi haka ba.
4. Wai a Hadisi aka rawaito Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ya na zuwa gidan wata mata mai suna Ummu Haram a Quba, ya kwanta a cinyarta ta na cire ma sa kwarkwata.
Sai Mallam Abduljabbar ya ce wannan karya ne, tatsuniya ce, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam bai taba yin kwarkwata ba.
5. Wai a Hadisi aka rawaito, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ya sa a yanka matasa dari bakwai 700 yankan rago, lokacin yakin Khaibar, sai Mallam Abduljabbar ya ce wannan karya ne kuma tatsuniya ce.
6. Wai a Hadisi aka rawaito Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ya tura Sahabban sa su je su yi fashi da makami, sai Mallam Abduljabbar ya ce wannan karya ne, tatsuniya ce.
7. Wai a Hadisi aka rawaito Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ya na saduwa da matan sa su Tara(9) ko goma sha daya (11) kullum sau biyu, sai Mallam Abduljabbar ya ce wannan karya ne, tatsuniya ce.
Allah ya baku sa'a masubin bayan gaskiya daga cikinku
ReplyDelete