Shin Da Gaske ne Imam Ali (A.S.) Yayi Shuru Bai Bawa Sayyada Fadima Kariya ba ???Gareku Ƴan Shi'a.....!!

 





Daga cikin Ishkalai da Shubhohin da waɗanda suka saɓawa ƴan Shi'a suke yi game da Mazlumiyyar Sayyida Faɗimatuz Zahra (a.s) , sukance : 

In har da gaske an kai hari gidan Sayyida Faɗimatuz Zahra (a.s.) har ta kai ga an daketa, me yasa Mijinta Ali bin Abi Ɗalib bai yi wani abu na bata kariya ba ? Tare da kasancewarsa jarumin da babu kamarsa , ko kuna nufin Ali (a.s.) ba Jarumi bane ? Ko ya nuna rashin kishi ta yadda ya kasance bai iya yin komai ba ana cutar da Matarsa a kan idonsa ? Ya akayi ya bari aka yi zalunci a kan idonsa bai yi komai ba ? Shin wannan ba suka bane ga haƙƙinshi ?


AMSA :


Zamu iya warware wannan Shubha da amsoshi mabanbanta , daga mafiya muhimmancinsu sune :


1 . Shin Usman bin Affan (Khalifa na Uku) Rago ne har da ya bari aka sari Matarsa akan Idonsa kafin a kasheshi ? Wani cikin makasansa ya dinga taɓa mazaunan matarsa yana cewa suna da girma amma Usman ba yi ko gezau ba , yana hana mataimakansa su bashi kariya har aka kashe shi a cikin gidansa , kamar yadda Aɗɗabari ya kawo a cikin Tarihinsa Juzu'i na 2 Shafi 421 , inda yake cewa : 


وجاء سودان بن حمران ليضربه فانكبت عليه نائلة ابنة الفرافصة واتقت السيف بيدها فتعمدها ونفح أصابعها فأطن أصابع يدها وولت فغمز أوراكها وقال إنها لكبيرة العجيزة وضرب عثمان فقتله.......(تاريخ الطبري - الطبري - ج ٣ - الصفحة ٤٢١)

Ma'ana : 

Sai Sudanu bn Hamran yazo domin ya sareshi (Ya sari Usman) , Sai Na'ilatu Ƴar Alfarafida matar Usman ta sa hannu ta tare Takobin, sai ya sareta a yatsunta da Takobin , sai ta juya , daga nan sai ya matsa kwankwasonta  (kamar yanda ake in za'a siyi Dabba) yace : Wallahi tana da manya manyan Mazaunai , sai kuma ya sari Usman da Takobinsa ya kashe shi .


Ka duba Tarihin Ibnu Khaldun da Albidaya Wannihaya da Alkamilu Fit Taarikh duk sun kawo wannan maganar  yayin da suke bayanin yadda aka kashe Usman bin Affan .


Ibnul Athiir yana Faɗa a cikin Alkamilu yana cewa :

Yayin da ƴan zanga-zangar nan suka ƙona ƙofar Gidan Usman suka shiga ciki , sai mutanen gidan suka hargitse shi kuma yana Sallah , daya idarr sai yace musu ya haramtawa yaransa da suke gidan su yaƙe su , su bari a kasheshi domin Annabi ya yi masa wani Alƙawari dan haka zai haƙuri da duk abinda zai sameshi . Ga Nassin dake cikin Alkamilu Fit Taarikh:


فلما رأوا ذلك ثاروا إلى الباب، فلم يمنعهم أحد منه، والباب مغلق لا يقدرون على الدخول منه، فجاؤوا بنـار فأحرقوه والسقيفة التي على الباب، وثار أهل الدار، وعثمان يصلي قد افتتح طه فما شغله ما سمع، ما يخطئ وما يتتعتع، حتى أتى عليها، فلما فرغ جلس إلى المصحف يقرأ فيه، وقرأ : آلَّذِينَ قَالَ لَهُمُ النَّاسُ إِنَّ النَّاسَ قَدْ جَمَعُواْ لَكُمْ فَاخْشَوْهُمْ فَزَادَهُمْ إِيمَاناً وَقَالُواْ حَسْبُنَا اللّهُ وَنِعْمَ الْوَكِيلُ. فقال لمن عنده بالدار : إن رسول الله صلى الله عليه وسلم قد عهد إليّ عهداً فأنا صابر عليه، ولم يحرقوا الباب إلا وهم يطلبون ما هو أعظم منه، فأحرّج على رجل أن يستقتل أو يقاتل". (الكامل في التاريخ لابن الأثير ج2 ص17)


Abun tambayar anan shine : Me yasa Usman bin Affan bai bawa Matarsa kariya ba musanman lokacin da Sudanu Bn Hamran yake taɓa mutuncin matarsa a kan idonsa ? Ko shi matsoraci ne ? Ko baya kishinta? Tare da cewa akwai manyan yaransa da suke kan katanga suna ta Harbin Yan zanga-zanga ta saman katanga , kuma yasan da zuwansu tun kafin kwana 40 yana da ikon ya ɗauki mataki ko da ta hanyar fita da iyalansa ne a lokacin da ake musu ƙawanya , amma shi Imam Ali (a.s.) an kawo masa hari ba shiri ba zato .


Tayu anan ku bawa Usmanu Uzuri da cewa Manzon Allah (saww) ya bashi labari da abinda zai faru , kuma yace masa yayi haƙuri da duk abinda za'a masa kamar yanda kuka rawaito .

Anan muma sai muce muku : Me yasa baza ku bawa Imam Ali (a.s) irin wannan Uzurin ba sanda aka kawo hari gidansa ???


2 . Tun asali ma wanene yace muku Imam Ali (a.s) ya zauna bai bada Kariya wa  Sayyida Faɗima ba ? 

Tabbas Imam Ali (a.s) ya fito tun bayan da yaji kiran Sayyida Zahra (a.s) a bakin ƙofa kuma ya daki wasu daga cikinsu wasu kuma suka gudu , Duba Littafin Sulaim bn Ƙais Shafi na 387 , za kaga yana cewa :


فأخذ بتلابيب عمر وطرحه أرضا ووجأ أنفه ورقبته وجلس على صدره وهمّ بقتله لولا أنه تذكر عهد رسول الله (صلى الله عليه وآله) فقال له: "يا ابن صهاك! والذي أكرم محمدا - صلى الله عليه وآله - بالنبوة؛ لولا كتاب من الله سبق وعهد عهده إليَّ رسول الله لعلمتَ أنك لا تدخل بيتي". (كتاب سُليم بن قيس الهلالي ص387).


Ma'ana: Sai Ali ya cafki gefen rigar Umar bin Khaɗɗab ya bugashi da ƙasa kuma yayi masa rauni a hanci da wuyansa, sannan ya zauna a akan Ƙirjinsa yana mai nufin kasheshi , ba dan ya tuna wasiyyar da Manzon Allah (saww) yayi masa ba , sai yace dashi : Yakai ɗan Sihak! Na rantse da wanda ya girmama Muhammadu da Annabta , ba dan Alƙawari da Wasiyya data gabata daga Allah  da kuma Alkawarin da Manzon Allah (saww) yayi min , da ka san cewa ba za ka shigo gidana ka zauna lafiya ba .


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post