[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Fassara Shi'anci a matsayin Mazhaba ko ƙungiya na daga cikin kwamɓale da Kuskuren da mutane suke yi , abun takaicin ba iya wanda ba ƴan Shi'a ba ko game garin ƴan Shi'a ke haka , har da ɗaliban ilmi akan samesu da wannan zamiyar akan ma'anar Shi'ancin , kai har Malamai akan samu da kiran Shi'anci da Mazhaba , wanda mafi kyan abinda za'a fuskantar da maganar su shine ; Suna yin rangwamen amfani da kalmomi ne shi yasa suke kiran Shi'anci da Mazhaba , in ba haka ba kai tsaye za'a ce sunyi kuskure babba ( Alkamalu lillahi ) .
MENE MA'ANAR MAZHABA ?
Kalmar mazhaba kalma ce Balarabiya da ma'anarta a tsurar larabcin shine " Matafiya " kuma ba wannan ma'anar mutane suke nufi da Shi'anci ba da sai muce da sauƙi , suna nufin ma'anar Isɗilahi ne ( Jurisfurudence Termilogy ) a ma'aunin Mazhabobin Fiqhu kamar Malikiyya da Shafi'iyya .
A isɗilahi kuwa (Wajen Malaman Fiqihu Na Ahlussunna Wal jama'a ) :
Mazhaba tana nufin abinda Mujtahidi ya fito dashi na daga hukunce hukuncen Shari'a masu fai'idantar da zato . Shi yasa suke cewa : Mazhabar Maliku Ko Shafi'i , ma'ana abinda Maliku ya tafi akansa na hukunci ko abinda Shafi'i ya tafi akansa na hukunci , amma Shi'anci fa ? A'a !
Domin Shi'anci ba mazhaba bane kuma ba ƙungiya bane kamar yanda wasu suke ɗaukar sa a matsayin Ɗai'ifa , ko Ɗariƙa kamar yanda Ɗariƙun sufaye suke duk ba haka bane al'amarin.
TO MENE NE SHI'ANCI ???
Ga duk wanda yake da ko da guntun sani ne game da Shi'anci , yasan Shi'anci wani gamammen tsari ne da yake ɗauke da Aƙida , Fiqhu (Furu'a) da kuma ɓangaren Akhlaq , wanda wannan shine ma'anar Addini gaba ɗayan sa , shi yasa in kaso kace: Shi'anci shine Musulunci haka nan Musulunci shine Shi'anci ba tare da banbanci ba , amma fa ingantaccen Musulunci na asali ba na jeka nayika ba .
In ka ɗauki Al-Kafi , Littafi Mafi girma a gurin Shi'a a yanzu , za ka samu ya rabu kashi Uku ; Usulul Kafi (Aƙida) , Furu'ul kafi (Fiqihu) da kuma Raudatul Kafi na daga abubuwan da suka shafi Akhlaq da sauran su , kuma wannan shine Addinin Musulunci gaba ɗayan sa .
Inda Shi'anci Mazhaba ce da ba za ka samu Aƙida a cikin sa ba , kamar yanda Mazhabar Malkiyya ko Hanafiyya take misali , Shi yasa za kaga mabiya Mazhabobi huɗun nan suna da wasu makarantu na Aƙida na daban da suke bi ( kamar Ash'ariyya ko Maturidiyya ) , ɗan ɗarikar sufaye kuma yana bukatar Mazhaba da kuma makarantar Aƙida a tare , to amma ɗan Shi'a fa ? Shi baya buƙatar komai daga ko ina sam , saboda yana da ( Manzuma Kamila Mutakamila ) Shi'anci sha kundum ne .
Wai ma ya za'a yi Ai'mmatu Ahlul baiti suna ce mana ; mune magadan Manzon Allah kuma muna fassara su da iya Fiqhun Mazhaba ! Anya bamu tauye musu matsayi da martaba ba kuwa ? Imam Ja'afarussadik ba iya Fiqhun Annabi kawai ya gada ba , ya gaji Aƙida da Akhlaq da duk wani ilmi da bama tunani , to amma sai mu takure shi cikin Mazhabar Fiqhu kawai ! Ai abun kunya ne ma ace Maliku ɗan Anas na da Mazhaba kuma ace Ja'afarussadiƙ (a.s.) ma Mazhabar Fuqhu gare shi kawai ! Wuce nan wallahi .
Don haka , maganar gaskiya Shi'anci ba Mazhaba bace ba kuma ƙungiya bace kamar yanda wasu suke ɗauka ko suka maida Shi'a , asali ma maƙiyan Shi'anci ne suke jifan Shi'anci da wannan fassara suce masa ; Mazhabar Ja'afariyya ko ƙungiya ko kuma wani Addini daban ba ma Musulunci ba , sai mu kuma muka ara muka yafa muke kiran kan mu da haka , kamar ma mun yarda da abinda suka ɗauke mu kenan , shi yasa aka samu wani Farfesa yake da'awar Shi'ancin Aƙida daban Mazhabar Ja'afariyya ma daban ! Abun dariya da takaici !!!
In ka ɗauki Shi'anci a matsayin Mazhaba kamar Malikiyya Ko Hambaliyya ka tauye shi baka ba shi haƙƙin sa ba , kamar ka ɗauki Farfesa ne ka dawo dashi aji ɗaya na Firamare ne . Shin baka ga babu wani ɓangare ko mazhaba ko ƙungiya ko ɗariƙa da ta Mallaki abinda Shi'anci ya mallaka ba ? To tayaya kuma za su zama a mataki ɗaya da sunan Mazhaba ko ƙungiya ? أين الثرى من الثريا .
Banbanci tsakanin Shi'anci da Mazhaba kamar banbancin babu da akwai ne ko banbancin sama da ƙasa .
In kai ɗan Shi'a ne ya zama wajibi ka kasan kana da abinda babu wanda ya mallake shi duk Duniya , In Aƙida ce ba'a fika ba wallahi , in Fiqihu ne kaine gidan sa ko anƙi ko anso , in Akhlaq ne da Tazkiyatunnafsi babu wanda ya isa ya kai Ahlul baiti kowaye shi ! Kaje ka buɗe Mafatihul jinan kawai ya ishe ka tsarkake Ruhin da za ka zama babban Waliyyi , babu inda za ka samu tsarabar manya manyan Addu'oi kamar gidan Shi'a wallahi kaje ka bincika ka gani ,Muke da Sahifa Sajjadiyya (زبور آل محمد ) .
Don hakane muke cewa ; Shi'anci ba Mazhaba bane , ba ƙungiya ba ce , ba kuma wani yanki na Addini bane , Shi'anci Addini ne gaba ɗayansa a dunƙule , ina nufin Addinin Musulunci na asali ba na bogi ko baba rodo ba .
ولما رأيت الناس في الدين قد غووا
تجعفرت باسم الله فيمن تجعفروا
ودنت بدين غير ما كنت داينا
به ونهاني سيد الناس جعفر
فقلت فهبني قد تهودت برهة
وإلا فديني دين من يتنصّر