Shekaru 7 Da Waki’ar Buhari A Zariya; JAGORA YA GANA DA IYALAN SHAHIDAI KASHI NA 4

 


* JARABAWAR DA MUKA GANI ALAMA CE TA CEWA ANA KAN HANYA


- Inji Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Ranar Lahadi 11/12/2022 (17 Jimadal Ula, 1444) Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da ba’adin Iyalan Shahidai kashi na hudu a gidansa da ke Abuja.

Yayin ganawar, wacce ta kasance bangaren tunawa da Waki’ar Buhari na kisan-kiyashin Zariya a shekarar 2015 karo na bakwai, Jagoran ya bayyana cewa waki’ar ba komai bane, face jarabawa wanda ke nuna cewa ana kan hanyar Allah Ta’ala. “Wannan jarabawa da muka gamu da ita a tafarkin Allah, alama ce ta cewa ana kan hanya, domin haka aka yi ma na farko, kuma babu makawa hanyar kenan, babu wata bayan ita. Hanya ce ta sadaukarwa, wanda sadaukarwar nan ne ke daukaka wadanda suka sadaukar, kuma da sadaukarwarsu ne wasu za su amfana wajen ganin al’amari ya tabbata.”

Shaikh Zakzaky ya bayyana waki’o’in da suka gabaci na Buhari da wadanda suka biyo bayanta a matsayin nufin makiya na ganin bayan Harkar Musulunci, inda yace: “duk abu daya ne, yunkuri ne na ga cewa an kawar da wannan Da’awa kawarwa na har abada, ya zama an gama kenan. Kuma sun dade suna wannan tunanin, sun shekara fiye da 35 suna kimtsa yin wannan aikin. Kullum kuma tunaninsu kenan, cewa akwai wani lokaci ne da za su dira mana sai su kashe kowa da kowa, sai su ji tsit. Ba za a sake jin motsinmu ba, an gama.”

Yace: “idan ma zai yiwu su iya hakan, to suna da bukatar kuma ya zama suna da wata na’ura wanda za su fitar da tunawa da mu a zukatan mutane, tunda in dai har mutane za su tuna mu, to abin zai dawo danye, abin na nan kenan. To kuma basu da wannan na’urar. Kuma randa duk aka ce wani ya fito yace lallai ba mafita ga wannan al’umma sai komawa ga addinin Allah. Mutane za su ce ah, wannan maganar da kake yi ai irin na mutanen nan ne da karkashe su. Tunda yake Da’awar kenan dama.”

Jagoran ya nuna mamakinsa ga wasu da har yanzu suke cewa tare hanya ne dalilin kisan kiyashin da aka yi a Zariya, bayan manyan kotuna guda uku daban-daban sun musanta wannan zargin sun wanke ‘yan uwa daga shi. Yace: “Har yanzu ni abin da yake bani mamaki, sai suce wai an tsare hanya ne. Ashe idan an tare hanya a kan budewa mutane wuta ne a karkashe su?”

Sayyid Zakzaky ya kuma nuna takaicinsa kan yadda mai Sakataren Gwamnatin Kaduna yace sun bizne mutane 347 a rami. Yace: “Tunda shi mai magana da yawun gwamnati ne ya je ya ba da shaida (a gaban Kwamitin da suka kafa), ka ga ba za su iya kankare wannan ba.”

Shaikh Zakzaky yace: “To wa ya ce muku ku bizne mutane? Bisa shari’a, a bisa ka’ida wa ke bizne mamaci? Iyalansa ne suke yi, kuma ana yi bisa ka’idar shari’a ne. To ya za ku je ku bizne Musulmi alhali shi Musulmi ana masa wanka, ana saka masa likafani, ana masa sallah!”


Ya cigaba da cewa: “ba a ce ka haqa rami ka bizne mutum sai ka masa addu’a kawai ba, an ce ana masa wanka ne, a saka masa likafani, a yi masa sallah, bisa koyarwar addini. Kuma baka da hakkin yin wannan, wanda yake waliyin mamaci shi ke da hakki ba kai ba.”

Yace: “Shiri ne da suka dade suna shiryawa, sun dade suna yin abin, tun ma mulkin Shagari, lokacin suka fara tunanin ya za a yi da mu ne. To da mulkin soja suka zo suka fara tunanin a kawar ne kawai, ana ta kirfa yadda za a kawar, kawarwar kuma shine za a yi amfani da karfin tsiya ne, a shirya wannan a shirya wannan.

“Wasu suka ce yadda za a yi a kurda ne a yi zagon kasa. Sai aka kurda din, sai bai yiwu ba. Sai aka ce to tunda abin ya ki, a yi ba sani ba sabo kawai a kawar. In an kulla wannan ya kwance, in an kulla wannan ya kwance. To shine har aka yi wannan shirin da aka yi na waki’ar Quds (2014), shirin yin gaba daya ne shima, don bayan kisan da suka yi ranar Juma’a, ranar Asabar ma sun yi gagarumin shiri, sun kamo hanya ma, sai lokacin ya zama Gyallaesu ta cika makil da mutane har da baki daga waje, kuma da yake suna da masu basu labari suka ce gaskiya wajen makil yake da mutane ga ‘yan jaridu kuma da aka gayyato wanda ana taron manema labarai a daidai lokacin, har sun kamo hanya za su zo, sai suka koma. Sai ya zama bayan Asabar din Lahadi kuma aka yi karamar Sallah.”

Shaikh Zakzaky ya cigaba da cewa: “Wadannan (Gwamnatin) suna hawa sai suka yi karin kumallo da mu, da mu suka fara, kamar dama suna jiran su fara da mu ne kafin ma su yi wani abu, kila abin da aka shardanta musu kenan, kuma suka daukawa iyayen gijinsu alkawari cewa sai sun ma kawar kafin ma su yi wani abu. Don haka ma aka dade ko ministoci ba a nada ba ana jira a kammala aiki, aiki ya ki kammaluwa, an yi yunkuri daban-daban, wasu mun sani wasu bamu sani ba, amma dai basu cimma nasara ba.”

Yace shine suka ce a yi ta manya-manya ta kare, a ka yi ba sani ba sabo kawai. “An rutsa da garin ne, duk hanyoyin da ke shiga Zariya sun tare ko ina suna kashe duk wanda suke tsammanin dan uwa ne. Ya ishe su kawai su ga sister da hijabi a cikin mota, to duk wadanda suke cikin motar sun mutu, ko su waye su.” Inji Jagora (H)

Yace: “Inda Allah ya tozarta su, da aka tambaye su meye dalilin da kuka yi wannan kashe-kashen? Suka ce an tsare mana hanya. Shikenan dalilin? To sai kuma shi Madugunsu yace an yi gwamnati a cikin gwamnati. Yauwa to ka ji maganar. Wato gwamnati guda biyu ne a kasar, yana da tasa, kuma ga wata daban, to zai kawar da wata daban.”

Shaikh Zakzaky yace: “To ai tun ranar da Iblis ya qi yi ma Annabi Adamu (AS) sujada, tun rannan aka yi gwamnati biyu; da gwamnatin Allah da ta Iblis. To zan tambaye ku tsakaninku da Allah, Gwamnatin Nijeriya ta waye? In wani ya isa yace mana ta Allah ce. Ya fada mana ta inda ta zama ta Allah din, ta ina ta san da dokan Allah din? Ita bata ma yarda akwai Allah din ba.” 

Yace: “Da yake akwai wanda yake ta surutu, kun san shi Zanqalelen baya magana, amma shi dan Tsigigin yana magana. To dan tsigigin ne ya fito karara yana cewa, wai ba dole ne a bi dokar Allah a Nijeriya ba, amma dole ne ka bi dokar kasar.”

Sayyid yace: “To Allah Shi ya halicci sama da kasa, Shi ya halicci mutane Ya dora su bisa doron kasa, kuma dokarSa ce ta zama dole a bi. Dokar mutum idan ta saba ma ta Allah to bata hau kanmu ba.”

Ya cigaba da cewa: “Kuma su kan ce wai mu bama bin doka. Nace wawayen banza wawayen wofi! Wa ke bin doka idan ba mu ba? Ai doke muke bi. Cewa muke idan doka ta sabawa ta Allah, bata hau kanmu ba. Ku fadi wannan maganar mana. Amma sai su ce ba a bin doka… An ce maka dokar da ta saba da ta Allah bata hau kanmu ba. Ba ma bin doka kenan? Dokar wa muke bi? Ta Allah. To, Dan Adam yana da hakkin ya yi dokar da ta sabawa ta Allah? Ina yake da wannan hakkin? Shi kansa an yi shine, kuma kasar da yake zaune a kai wani ne ya yi.”

Shaikh Zakzaky ya jaddada cewa: “Don a sani, idan aka ce ga doka da ta sabawa ta Allah, sai bamu bi ba, to mun bi ta Allah ne. Allah muka bi. Idan kuna ganin ya kamata mu bi dokar ne, sai ku yi dokar da bata sabawa ta Allah ba. In bata dabawa ta Allah ba shikenan.”

Da yake amsa ga ikirarin da Muhammad Bin Salman ya yi a kan cewa su suka biya kwangilar kawar da Shi’a da dakile kafa Gwamnatin Musulunci irin ta Iran da Shaikh Zakzaky yake kokarin yi. Jagora ya bayyana cewa: “Ita Gwamnatin Musulunci ba mutum ne yake kafata ba, Allah ne yake kafata, kuma yana kafata a inda ya ga dama, da wanda ya ga dama, a lokacin da ya ga dama, kuma wani bai isa ya hana ba. Ba wani mutum ne sunansa Zakzaky zai kafa Gwamnatin Musulunci ba, Allah Ta’ala ne zai kafa da wanda ya ga dama, a inda ya ga dama, a lokacin da ya ga dama.”

Shaikh Zakzaky yace: “Sun yi abin da suka yi, sun yi kisan kai ne, kisan kan da Shaidan ya sauwala musu cewa idan suka yi shikenan bukatarsu ta biya. Idan dama makasudin abin da suka so shine su yi kisan kai, to shikenan sun yi, sun kashe mata da yara da kowa da kowa, har da masu ciki da iyalai, ba irin barnar da ba a yi ba. Idan shine makasudi an yi kenan. Amma ba shine makasudin ba, makasudin shine a kawar da al’amarin. To ya kawu?” Ya tambaya.

Jagora ya bayyana cewa dirarwa Harkar da makiya suka yi ya sa sun tambatsa ta, har yanzu suna nuna bukatar a bar Abuja a koma Zariya da zama. Yace: “ai yanzu ba Abuja ne kawai ba, ko ina ne ma, ba inda al’amarin nan bai shiga ba. Kuma habaka yake yi. Su kuwa ‘yan bakin ciki sai dai su mutu da bakin ciki din.”

Da yake magana da iyalan Shahidai, Jagora ya bayyana cewa: “Dacin Shahada din nan shi kansa yana da nasa matsayin. –Wato ka tuna da wanda aka rasa, kuma ka yi kuka ka ji zafi, to yana kambama lada. Amma in ka yi sai kuma ka mai da al’amari izuwa ga Allah.”

Yace: “Kuka ya zama lazim, mutum ya koka sai kuma ya yi addu’a yace Ya Rabbi na kawo maka kukana ne, ka sani game da ni abin da nima ban sani ba. Yauwa. Allah kake ma kuka.”

Shaikh Zakzaky yace: “Su (azzalumai) suna tsammanin in mun koka kamar su muke ma koka. Suna kuma tsammanin idan mun yi Muzaharori kamar muna rokonsu ne. Mu ba rokonsu muke ba. Ko da kun ji an ce ku yi kaza, ba yana nufin ana rokonku bane, ana fada muku abin da ya hau kanku ne, ku yi ko kar ku yi, amma wannan hanya ce ta isar da sako. Me yasa basu son (Muzahara)? Saboda sun san hanya ce ta isar da sako.”

A karshen jawabinsa, Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa: “Fir’auna ko dan Tsigigi ko Zanqalele karshensa na nan tafe, kuma karshen mummuna a nan Duniya. Kuma yadda ake tuna Fir’auna ake tsine masa, haka za mu rika tuna duk Fir’aunonin da suka yi mana barna muna tsine musu, ba za a manta da wannan ba. Kar su dauka ya fita ne, ina cewa mun rubuta shi da tawadar da baya kafewa, a muhallin da baya bushewa, ya dinga rayuwa kenan.”

Ya rufe jawabinsa da jaje da addu’a: “Muna ma wadanda suka rasa masoyansu jaje, da cewa a daure a yi hakuri, a kuma nemi taimakon Allah da dauriya. Sannan kuma wadanda suka ba da jinanensu muna musu fatan suna tare da rayayyu da ake azurtawa. Kuma su ma muna basu tabbacin cewa Insha Allah abin da suka ba da ransu a kai, a kanshi za mu tsaya kyam har mu cimma namu ajalin Insha Allah.”


@SZakzakyOffice

12/12/2022

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post