Shekara 7 da waƙi’ar Buhari: Hurras Na Azzahara Zone Sun Yi Gagarumar Muzahara A Dutsamma!!!.

 


—Bin Yaqoub Katsina.


Tun da farko dai ɗaruruwan Hurras almajiran Sayyid Zakzaky (H) na yankin Katsina da kewaye, (AZZAHRA ZONE) sun yi tsinke a garin Dutsimma da safiyar yau Asabar 17/12/2022 inda su ka gabatar da ƙwarya-kwaryan ‘Oriantation’ ga ma’aikatan na Hurras, wanda a taron Malam Dr. Jamilu Kankia ya gabatar da jawabi kan sanin makamar aiki da muhimmanta da shi. 


Malam Yaƙub Idris shi ne ya yi jawabin ƙarshe wanda ya ja hankalin Hurras ɗin da nusar da su nauyin da ke bisa kawukansu. Daga karshe wakilin ’yan’uwa na garin Dutsamma ya yi jawabin godiya.


Kammala taron ke da wuya sai gaba ɗayan tawagar Hurras ɗin su ka ɗunguma inda su ka hallara bisa kwalta su na ɗauke da hotunan jagora Sayyid Zakzaky (H) da ke nuna juyayisu na cika shekaru 7 da aiwatar da kisan ta’addanci wanda gwamnatin Najeriya ƙarƙashin umarnin shugaban kasa Buhari ta aiwatar a Zariya shekarar 2015. 


Har wa yau dai a lokaci guda wasu na ɗauke da kwalayen da aka rubuta ‘Free Zakzaky's Passport’ wasu kuma an rubuta ‘Release Zakzaky's Passport', ma'ana su na kira ga gwamnatin Najeriya ta gaggauta baiwa Sayyid Zakzaky (H) Passport dinsa domin fita waje neman lafiya.


Muzaharar wadda mafi yawanta Zallar Matasan Hurras ne na Jaishi Amirul Mumineen da kuma Hurras Re-enforcement, ta isar da saƙo da kuma ɗaukar hankalin al’ummar garin na Dutsimma, inda bayan an kwashe wasu awanni aka kammala lafiya inda wakilin Hurras ɗin na Azzahra Zone; Malam Yakub Idris ya rufe Muzaharar da jawabinsa. 


Ga wasu hotunan yadda tarukan biyu su ka gudana.


  #HMC

17Dec2022

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post