Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara A Karni Na Ashirin Da Daya (1)





[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]

✍️ Hussaini Fata


Duniya ba ta shedi wani mutum a duniyar hausa Fulani ba wanda kungiyoyin addinin Musulunchi suka hadu domin yaki dashi kamar sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ba, domin kowannen su yana da matsala da shi saboda wasu dalilai, kodai akan shehin su ko aqidar su ko kungiyar su


An fara jin muryar sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ne a karshen 1990s, inda shehin malamin ya fara kai hari janibin masu da'awar iyayen Annabi suna wuta, manzon Allah yana fitsari a tsaye, ba'a tawassuli da Annabi, da sauransu, inda shehin malamin ya shahara da martani mai gauni akan masu irin wannan aqidar da dalilai na Ilmi, har  yana cewa; "Wadaran Addini in har ba zai tsayu ba sai an ta6a kimar Annabin da yazo da addinin"


Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara mutum ne kafaffe akan abinda yakai yakini akan sa, wanda baya yin shiru akan duk wata tawaya da ake jinginawa a janibin Allah (T) da Manzonsa, da sunan nassi ko ruwaya, hakan yasa ya samu matsala da wasu masu kiran shehin su da Allah da kuma masu cewa Allah yana da nauyi musamman idan yayi fushi, har al'arshi ma tana qara idan yayi fushi, ko kuma su ce Allah yana sakkowa daga wani waje zuwa wani waje, ko kuma suce wutar jahannama ba zata cika ba sai Allah ya sanya kafarsa a cikin ta sannan zata ce da ubangijin ta na cika yanzu, da sauran kurafat da aka cusa a aqidun Musulunchi kuma ake inganta su. Akwai wata ibarar sa da yake cewa; "Idan an ce muslim ne ya inganta sai muce ai ana yin Musulunchi tun kafin Muslim ya inganta wannan tatsunniyoyin"


A matsayin sa na wanda ake ganinsa sufi kuma bakadire a tashin farko, yayi kokari wajen tsaftace wasu al'adu a tafiyar gidan su na darika, inda ya nuna wasu tasarrufofi da akeyi a gidan su da sunan dariqa, ya nuna ba su da inganchi a addini, don haka ya chanchanchi a daina su, hakan yasa anan ma ya samu matsala da wasu daga cikin 'yan'uwan sa na jini, har wasun su suka rinqa barazanar kashe shi tun kafin a samu wasu daga wajen gidan nasu suyi da'awar sai sun ga bayansa (kashe shi) har gidan mahaifinsa aka hana shi shiga kuma ya hakura babu yanda ya iya


Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ya fahimchi hatsarin da yake fuskanta sosai da gaske, musamman daga wadanda yake wargaje aqidojin su da dalilai, har ya kai yana cewa "Kana tunanin ban shirya ma hakan ba?" "Ko kuwa idan ban shirya wa mutuwa ba zan yi abinda nakeyi?" kuma an sha kai masa hari ta fuskoki daban-daban Allah yana tsallakar dashi, ta hanyar bashi guba, da yin siddabaru akan abin hawansa da sauran su


Farin jininsa ya ta yaduwa tsakankanin al'umma da suka hada da 'yan boko, daliban ilmin addini, shahararrun mutane, a cikin kasa da wajen ta, duk da an hana sanya karatuttukansa a gidan radio amma duk da haka sai da farin jininsa ya fantsama duniya. Shehin malamin ya kasance mai gina almajiransa akan bahasi mai karfi, da basu damar naqadi yayin bijirar da dalilai, almajiransa sun sha ankarar da shehin malamin na su a majlisin karatuttukansa na "Al'ababil" ko "Mukaddimar Al'azifa" inda yake kar6ar gyaran su cikin dadin rai yana musu jinjina.


A farkon shekarun 2000s an ji amon shehin malamin yana kai kariya a janibin Ahlulbait (A) da dukkan karfinsa har yana nunawa duniya 6alo-6alo shi yana tare da su, har yana sukar wasu magabata ganin yanda sukayi mu'amala da su (Ahlulbait) a zamanin su, hakan yasa wasu suke kallon sa a matsayin mai zagin sahabbai, ko wanda yake kokarin baje kolin shi'anchi, har ma an yi hira dashi a shafin BBC hausa inda ya nunawa duniya cewa rikichin dake tsakanin Shi'a da Sunnah kaso saba'in da biyar cikin dari 'yan Shi'a sun fi gaskiya


Zamu cigaba insha Allah

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post