@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
INGREDIENTS:
1. Lemon grass
2. Citta (ginger)
3. Tafarnuwa (garlic)
4. Cardamom (habbahan)
5. Cumin
6. Cinnamon (girfa)
7. Kanumfari (clove)
8. Na'a Na'a (mint)
9. Habbatus sauda (black seed)
10. Zuma (honey)
11. Nutmeg (gyaďar miya)
12. Top tea, green tea, sai ginseng in kina so.
Ki nemi dai ganyen shayi da kike amfani da shi ki sa kawai.
PROCEDURE
Shima kamar yanda na yi bayanin sauran ne mace zata nemi dukkan abubuwan including tafarnuwa, zata iya saka danye ko kuma busashshe su dahu tare. Kuma bayan ya gama dahuwa ba zaki ji kamshin tafarnuwar ya fito ba sam. Sai nutmeg shima ďaya zuwa biyu ya isa ki fasa ki cire bawon ki zuba abun ciki.
Domin shi ba kowa ne ke son kamshinsa ba shi yasa guda daya ya isa yanda zai hade da sauran ba a ji shi ba. Shima wannan yana gyara hailar mace, idan ke mai yawan ciwon ciki ce in kina haila to kina fara wa ki dafa irin wannan shayin kina sha yana dumama jikinki zai rage miki ciwo. In mace ta jure shan shi yana kashe infection da sa kamshin gaba. Habbatus sauda garin ne zaki saka su dahu tare.
Lemon grass na manta sunansa da hausa amma shi bashi da wahalar samu. Yawanci a jikin shukan gida masu flowers suke fito wa. Idan mutum na fama da matsalar disashewar murya ko kullum cikin mura to shan wannan zai gyara masa su in shaa Allah. Sannan in kin dafa zaki iya busar da su aqallah ki dafa sau biyu ko ma uku kafin ki zubar. Iyaka ki cire kanunfari haka, da ganyen shayin, amma in da yawa ne abubuwan ciki sun fita zaki iya zubarwa.