Kisan kiyashin Zaria |
Kashi Na 1:
Daga Littafin: KISAN-KIYASHIN ZARIA DA ABUBUWAN DA SUKA BIYO BAYA
WALLAFAR: Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H)
SHIMFIƊA:
Kimanin shekaru goma sha ɗaya da suka gabata, a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Umaru Musa Yar’Adua, gwamnatin Nijeriya bisa umurnin Amerika da Isra’ila ta yi shiri na musamman don murƙushe Harkar Musulunci a Nijeriya ta hanyar kashe Jagoranta da tarwatsa dukkan dandazon mabiya Harkar ta Musulunci.
A wancan lokacin, sun tsara cewa za su jefa Bom ne a gidan Shaikh Zakzaky, sai ya zama cikin sauƙi sun kashe shi da dukkan iyalansa. A yayin da mabiya suka fito da nufin yin Muzaharar Allah-wadai da wannan mummunan aikin kuma, sai su buɗe wuta a kansu, kamar dai yadda suka yi ga wasu mutane da suka raɗawa suna ‘yan ƙungiyar Boko Haram a jihohin Arewa maso-gabashin Nijeriya, a shekarar 2009.
Wannan yunƙurin na gwamnatin ‘Yar Adu’a ya bi ruwa ne bayan da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya samu cikakken rahoton zaman sirrin da suka tsara aiwatar da wannan ɗanyen aikin, tare da kwafin takardar sirri (Blueprint) na gwamnati kan yadda ta tsara za ta aiwatar da kisan-kiyashin daki-daki. Shaikh Zakzaky bai yi jinkiri ba wajen shelantawa duniya halin da ake ciki, a wajen Tafsirin Alqur’ani na watan Ramadanan 1430 a FIC, Zariya.
Duk da fallasa cewa jami’an tsaro na shirin yin kisan-kiyashi a kan ‘yan uwa Musulmi da Shaikh Zakzaky ya yi a wannan lokacin, bai hana jami’an tsaron su buɗewa masu Muzaharar nuna goyon bayan Falasdinawa wuta a Zariya ba a ranar Juma’ar qarshen Ramadan ɗin wannan shekarar, wacce ta dace da kwanan watan18/9/2009. Inda suka kashe mutane biyu, tare da jikkata gomomi a daidai ƙofar doka, Zariya.
Bayan mutuwar Umaru Musa ‘Yar Adu’a a ranar 5/5/2010, da yake kamar yadda Shaikh Zakzaky ya sha faɗa ƙarara a jawabansa da hirarrakinsa da ‘yan jaridu, cewa, wasu ayyanannun ƙasashe ne suke da nufin a kashe musu shi, a kuma kawo ƙarshen Harkar Musulunci a Nijeriya, kasancewar suna kallonta a matsayin barazana gare su da manufofinsu na sake mamaye qasar da ɗebe arzikin cikinta. Don haka sai kwangilar kashe Shaikh Zakzaky ta komo hannun shugaban qasa Goodluck Ebele Jonathan, wanda shi ne ya gaji ‘Yar Adu’a bayan mutuwarsa.
Da farko, ƙasashen da ke nufin ganin bayan Shaikh Zakzaky da da’awarsa, wanda suka haɗa da Amurka da Isra’ila, sun ba da kwangilar aikin ne ga wani Baturen Birtaniya, mazaunin ƙasar Amurka, mai suna Patrick Williams, wanda aka ce yana da kamfani na musamman don yin kisan mummuke ga duk wanda ake buƙatar kashewa a Duniya.
Patrick ya samu cikakken iko na yin amfani da wasu jami’an tsaron Nijeriya a duk sanda yake buƙata, inda suka riƙa shirin su harbe Shaikh Zakzaky (H), musamman a kan hanyarsa ta zuwa Husainiyyah Baƙiyyatullah inda yake bayar da karatun Tafsiri da Nahjul Balagha da sauran munasabobin addini. Sai dai, hakan ya ci musu tura, a yayin da a ranar Mauludin Manzon Allah (S), na shekarar 1433 (19/2/2012), Shaikh Ibraheem Zakzaky ya fallasa wannan shirin ya kuma yi wa Patrick da waɗanda suka ba shi aikin albishir da rashin cikar burinsu.
Shaikh Zakzaky (H) yake cewa: “Duk ranar da Allah ya ƙaddara min ajali, ya kuma zama Shahada ya ƙaddara min, kuma ya zama kai Patrick kai ne makashina, zan yi wa kaina kyakkyawan albishir, in ce Alhamdulillah! Na godewa Allah da ya zama kafiri tantiri irinka ne aka ba shi kwangilar kashe ni. Albishirin ka! Kai kuma ba za ka rayu a bayana ba, ko shekara ma ba za ka yi ba. Wannan ma idan ka ga an kashe ni ajali na ne ya yi, kuma ko a kashe ni ko in mutu, wani abu guda shi ne, addinin yana nan, ruhin addinin kuma yana nan. Shi wannan ba ku isa ku kashe shi ba!”
Daga baya, kwangilar kashe Shaikh Zakzaky da murƙushe Harkar Musulunci ta koma kai tsaye hannun shugaban ƙasa Ebele Jonathan tare da mataimakinsa Muhammad Namadi Sambo. Kamar yadda a wani jawabinsa a shekarar 2013 Shaikh Zakzaky yake bayyana cewa: “To, kuma yanzu sun sanar da shi shugaban qasa da mataimakinsa, duk an sanar da su, kuma sun yarda sun saka hannu a kan sun amince za a kawar da Al-Zakzaky.”
Don haka ya zama dare da rana, kowane lokaci, musamman a ƙarshe-ƙarshen mulkin Jonathan, Shaikh Zakzaky (H) na faman tsallake yunqurin kisa ne daga jami’an tsaro. Har ma a ranar bikin Nisfu Sha’aban ɗin shekarar 1435 (2014) yake cewa: “Kullum cikin tsallake hari muke daga waɗannan miyagun mutanen. Yunƙurinsu kullum shi ne ya za a yi su ga sun kashe mu… To, amma ran mu ba shi a hannunsu, yana hannun Allah ne. Allah Ta’ala ne mai rayawa. Da ace ranmu na hannunsu ne ai da tuni sun zare shi, tun da tuntuni suna ta faman baƙin ciki, ga abu ba su so, ga shi yana ta havaka!.”
A ranar Juma’ar qarshen watan Ramadan ɗin shekarar 1435 (27/7/2014), a ƙoƙarinsu na murƙushe Harkar Musulunci, sojojin Nijeriya sun dira a kan almajiran Shaikh Zakzaky a daidai P.Z da ke Zariya, a yayin da ake gudanar da Muzaharar nuna goyon bayan Falasdinawa, inda sojojin suka kashe mutane 34, cikinsu har da ‘ya’yan Shaikh Zakzaky na cikinsa su uku, waɗanda sun kama su ne da ransu da lafiyarsu suka tafi da su barikin Basawa, suka kashe su ta hanyar azabtarwa.
Sojoji, tun a wannan lokacin sun yi niyyar su samu dama ne da za su cigaba da kashe-kashe har su kai ga Shaikh Zakzaky, shi ya sa ma bayan sun yi wannan kisan-kiyashin, sun ta zura ido su ga ko mabiya Shaikh Zakzaky za su fito Muzahara don yin Allah-wadai da harin, sai su yi amfani da wannan damar wajen cigaba da kashe su, tare da bi gida-gida suna kisa da sunan suna neman ‘yan uwa Musulmin, amma wannan lokacin, sai Shaikh Zakzaky ya hana mabiyan nasa fita don yin komai. Aka yi janazar Shahidan da aka kashe kawai, aka yi zaman makoki aka sallami jama’a.
Duk da haka, sai sojojin suka riƙa yaɗa farfaganda da labaran ƙarya, cewa ‘yan uwa Musulmi suna shirin za su mai da martani ga sojoji a barikinsu, ƙaryar da ba ta samu wajen zama ba a ƙwaƙwalen waɗanda suka san Harkar Musulunci a tsawon shekaru fiye da 30 a matsayin tafiyar addini marar tashin-hankali ko neman faɗa da kowa.
A ranar 22 ga Muharram 1436 (14/11/2014), bayan kammala zaman juyayin Ashura, Shaikh Zakzaky ya ba da labari cewa: “Ɗazu abin da aka ce mana; an tara Sojoji a sansaninsu, an ce musu; Al-Zakzaky zai yi bore, saboda haka su zama cikin shiri komai na iya faruwa. To, me ya kawo sunan Al-Zakzaky kai da kake ‘Training’? Kuma in ya yi bore, ina ruwanka da boren? Na ɗauka idan ma wani abu ne, ba aikin ‘yan Sanda ba ne? Sai dai in Ɗansanda ya gayyaceka ka taimaka masa, amma Soja da Bindiga an ce mishi Al-Zakzaky zai yi bore ya zama cikin shiri, komai na iya faruwa.
“Wannan abin da aka gaya musu ɗazu kenan. Kuma aka ce su riƙe Bindigoginsu, yanzu haka Bindigogin na hannunsu, kuma suna nan yanzu cikin shiri. Kuma sun shigo (Zariya) motoci ne ba kaɗan ba. Tun kwanaki suna ta shigowa, har da inda aka ga mota goma da Turawa zalla a ciki, sun shigo sun je barikin Basawa shekaran-jiya wancan. Kuma yanzun mota goma, Mota 20 duk suna shiga. To, kuma duk ba za mu damu ba. Amma me ya kawo sunan Al-Zakzaky? Da yake shi Soja (a Nijeriya) ana mishi tarbiyyah ne da cewa; su mutanen gari sune abokanan gabansa. Shi za shi ya yi kisan kai ne kawai!!”
Shaikh Zakzaky ya cigaba da cewa: “To, wala Allah su zama cikin shirin, kila sun shirya suna da wani ‘Unit’ wanda zai sa baƙin kaya, ya je ya yi ta’addanci, su ce; to, ka gani, dama mun gaya muku. Daga nan kuma sai su shigo gari, su shiga kisan kai.”
Tun daga wannan lokacin, sojoji a ƙarƙashin mulkin Jonathan suka riƙa kai farmaki a kan Shaikh Zakzaky, a kowane lokaci suna da nufin su buɗe masa wuta, ko dai a kan hanyarsa ko kuma a gidansa. Haka ne ma ya sa wani lokacin sukan shigo cikin unguwar Gyallesu da tsakar dare, amma idan suka ga komai dare unguwar ba ta rabuwa da ‘yan uwa da suke aikin bada kariya ga Jagora, sai su juya a guje!
Har ya zama Shaikh Zakzaky ya tsallake yunƙurin kisa daga gwamnatin Jonathan fiye da sau 30 a lokuta daban-daban. Ta kai ma ga yakan canza hanya idan aka gano sun yi kwanton-ɓauna a hanyar da aka saba bi zuwa wajen karatu. Haka aka riƙa fama har zuwa lokacin da aka samu canjin gwamnati. Ya zama Shugaba Muhammadu Buhari ke mulki a ƙarƙashin jam’iyyar APC, a shekarar 2015.
A farko, kamar komai zai tafi lafiya kalau, bayan ‘yan watanni da hawansa, musamman bayan da wata tashar satilayit mallakar qasar Saudiyya, mai suna WISAL-TV, ta fitar da wani rahoto wanda a cikinsa ta gargaɗi hukumomin Nijeriya akan barin da suka yi Shi’a na yaɗuwa a ƙasar, ta kuma yi kira gare su da su daƙile yaɗuwar Shi’ancin, kawai sai aka fara ganin hare-hare a kan ‘yan uwa Musulmi, harin kusa da kisan-kiyashin Zariya shi ne harin Bom da aka turo wasu yara cikin masu Tattakin Arba’in ɗin Imam Husain (AS) daga yankin Kano, wanda ya yi sanadiyyar kashe mutum 23 da jikkata gomomin ‘yan uwan.
Bayan faruwar wannan harin, Shaikh Zakzaky ya ɗaura alhakin harin akan jami’an tsaro, bisa dalilan da ya bayyana a cikin jawabinsa na ranar Arba’in, wanda aka gudanar a ranar Alhamis, 3 ga watan Disambar 2015. Kuma ba a samu wata murya daga ɓangaren gwamnati ko jami’an tsaron ƙasar nan da ta musanta zargin da Shaikh Zakzaky ya yi a wannan lokacin na cewa jami’an tsaron ne suka kawo harin ba, sai kawai martanin da sojoji suka bayar kwanaki tara bayan wannan jawabin, wanda shi ne ‘Kisan-Kiyashin Zariya’.
Za mu cigaba.
📰Journalist
Dan Fudiyya
3 Dec 2022
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com