[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Bayan shelanta wannan ƙira nasa ya fuskanci tsangwama mai tarin yawa ta fuskoki da ɓangarori da dama, kama daga azabtarwa daga ɓangaren hukuma, da kuma matsin lamba daga dangi da makusantansa. A wani jawabinsa yana cewa; “Wani ma ya ce min “ba za ka koma Jami’a ka yi karatu ba!” (sai) na ce masa; to ai wannan aikin da kake so na yi akwai masu yi, amma wannan (Da’awa) da nake yi ba mai yi! Saboda haka gara wannan shi ma a tsaya a yi shi” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 18).
Kowa zai so sanin yaya aka yi Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) ya fara wannan Da’awa tasa, wato meye dalili, ko ya aka yi tunanin fara yin Da’awar ya zo masa?
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya sha amsa wannan tambaya ga ‘yan jaridu, yakan ce, shi a farko bai taɓa tunanin zai zama mai Da’awa ko ya zama malamin addini ba, tunaninsa shi ne in ya gama karatunsa na boko zai zama ma’aikacin gwamnati ne ko malamin jami’a, domin rayuwar ma’aikatan gwamnati da ta malaman jami’a tana burge shi, rayuwa ce ta natsuwa wacce ba hayaniya a cikinta, kuma shi yana sha’awar rayuwa ta kaɗaici da natsuwa, ba ya son a san shi ko ya zama wani fitaccen mutum, domin ba ya son hayaniya da ɗawainiyoyi da yawa.