Sayyidah Fatima Az-Zahra(AS) |
@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
- Mallam BaQeer...✍️
**TARIHIN FA'DIMATUZ-ZAHRA {S. A}**
An haifi Fatima al-Zahra (a.s) ne a ranar juma'a, Ashirin ga watan Jimada Sani, shekaru biyar bayan aiko Annabi. Bayan haihuwar Manzon Allah (s.a.w.a) ya amshi 'yarsa da farin ciki da amincewa, ya kuma sa mata suna Fatima.
An haifeta kuma ta tashi a gidan Annabci, ta tarbiyyantu a inuwar wahayi, ta kuma sha kaunar imani da kyawawan dabi'u daga Khadija.
Fatima ta kasance mai dauke da ruhin Manzon Allah (s.a.w.a) da dabi'unsa, don haka ta zama mai gado da kuma tsananin kama da shi, har ma A'isha ta taba cewa:
"Ban ga wanda ya fi kama da Manzon Allah (s.a.w.a) a rashin magana da kyauta fiye da Fatima 'yar Manzon Allah ba, a tsayuwarta da zamanta. Ta kasance idan ta shiga wajen Annabi (s.a.w.a) ya kan mike ya tarbe ta, ya zaunar da ita a wurin zamansa. Haka nan idan Annabi ya shiga gare ta, ta kan mike daga wajen zamanta ta tarbe shi, ta zaunar da shi a wajen zamanta(1)"
Allah Ya so Fatima ta fara yarintarta a wani yanayi mafi tsananin wahala da kuntatawa daga matakan da'awar Musulunci; kuma wanda mahaifanta suka fi shan wahala da cutuwa a cikinsa. Ga dai Kuraishawa nan na tilasta takunkumi tattalin arziki a kan Manzon Allah da danginsa daga banu Hashim da mayar da su saniyar-ware. A wannan lokacin ne aka tsare Manzon Allah (s.a.w.a) a Shi'abi Abi Talib tare da matarsa Khadija, 'yarsa Fatima da sauran musulmi.
Shekarun takunkumi sun wuce tare da matsanancin hali, har zuwa lokacin da Manzo (s.a.w.a) ya fita daga cikinsa tare da wadanda ke tare da shi alhali Allah Ya rubuta masa nasara da galaba. Khadija kuwa ta fita daga cikin shi alhali shekarun sun yi mata nauyi, gajiyar takunkumi da Matsalolinsa sun raunana ta. Wannan ya sa ajalinta ya gabato.😢
Allah Ya zabar mata MakwabtakarSa, inda ta rasu a wannan shekara, bayan 'yan watanni kuma sai Abu Dalib baffan Annabi (s.a.w.a), mai kariya da taimakon Musulunci; wanda Manzo (s.a.w.a) ya bayyana yadda ya yi rashinsa da fadarsa cewa: "Kuraishawa ba su fara matsamin ba har sai da Abu Dalib ya yi wafati(2)",ya rasu.
Hakika Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi bakin ciki kuma ya ji kadaici a saboda rabuwa da Khadija. Domin ya yi rashin Khadija matarsa, masoyiyarsa kuma mai taimakonsa. Kamar yadda ya yi rashin baffansa mai kariya gare shi; don haka ya kira wannan shekara da sunan Shekarar Bakin-Ciki.
Fatima, karamar 'yar Manzo (a wannan lokaci) ma ta rayu cikin wani bangare na wannan bakin ciki, ita ma ta yi makoki, don kuwa ita ma bala'in wannan shekarar ya taba ta; yayin da ta rasa uwa mai tausayi; alhali kafin nan ta koshi da kaunarta da lurarta, don haka (yanzu) ta lullubu da bakin-ciki da maraici.
Sanannen abu ne cewa dole ne wannan rasuwa ta girgiza Fatima don kuwa ta rasa mahaifiyarta, ta rabu da cibiyar kaunarta, don haka sai dacin rabuwa ya cika zuciyarta ya kuma girgiza ta.
Babanta Manzon Allah (s.a.w.a) ya dandana bakin-cikin Fatima; yayin da ya ga karamar 'yarsa na zubar da hawayen rabuwa, sai zuciyarsa mai tausayi ta yi kuna, jiyayyar nan tasa ta uba mai kauna ta gaskiya ta tabu, don haka sai ya kusanci Fatima don ya musanya mata abin da ta yi rashi na kauna da kusanci da kaunarsa da taushin zuciyarsa.
Hakika Manzon Allah (s.a.w.a) ya so Fatima kuma ita ma ta so shi; ya tausaya mata kuma ita ma ta tausaya masa. Babu wanda wanda ya fi Fatima kusa da shi kuma ba wanda yake so kamar ta. Ya sha jaddada wannan alaka a cikin hadisansa yana bayyana matsayinta a cikin al'ummarsa. Ga kadan daga cikin abubuwan da ya fadi dangane da ita;
"Fatima wani yanki ne daga gare ni, wanda ya fusata ta ya fusata ni(3)". da kuma cewa:
"Lallai Fatima wani yanki ne daga gare ni, (duk) abin da ke cutar da ita yana cutar da ni (4)".A wani wajen kuma ya ce:
"Ya Fatima, ashe ba ki yarda da kasancewa shugabar matan duniya ba, kuma shugabar wannan al'umma da shugabar matan Muminai.(4)".
Fatima na girma alhali kaunar babanta gare ta na girma tare da ita, tausayinsa a kanta na karuwa; kuma ita ma tana musanya masa wannan kauna, tana cika zuciyarsa da lura; don haka ya kira ta da Ummu Abiha (wato uwa a wajen babanta)(5)"..
Ta kasance tana ji da shi da tausaya masa irin tausayin uwa ga 'ya'yanta, tana kuma lura da shi kamar yadda uwaye mata ke lura da 'ya'yansu kanana, wanda hakan ya zamanto abin koyi ne na tsarkakkar alakar uba (da 'ya'yansa) wajen gina 'ya'ya da fuskantar da dabi'u da rayuwarsu, da cika zukatansu da kauna da tausayi. Hakika wannan alaka ta zama babbar abar misali a fagen renon 'ya mace a Musulunci da lura da ita, girmama ta da daukaka matsayinta.
Ina mai matuqar murnar taya ɗaukin masoya ahalin gidan annabin rahma murnar Samun Shumagabar Matan duk duniya da lahira. 🙏👏
#Writing by Mallam BaQeer...✍️