[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Masu Tahqiqi da Tadabburin Ayoyin Allah, irinsu Allamah Tabataba'i, sun tabbatar da cewa: A cikin Al-Qur'ani akwai Ayoyi fiye da Dari Ukku (300+), da suka kira Bil-adama zuwa ga Tadabburi, Tafakkuri, Hankaltuwa da Ta'aqquli wajen kokarin fahimtar Samuwa da Samammu.
Haka akwai Ayoyinda ke koyawa Annabawa Muhawara da Ihtijaji da Qa'idojin Mandiqi wajen kafa Hujja, ko Tunkude Shubuha, kamar fadar Mahallici cewa: " Kace Shin akwai wanda ya ke Mallakar wani abu daga wajen Allah idan yayi nufin Halakarda Almasihu Dan Maryam da Mahaifiyarshi? ". Haka fadar Allah inda yake cewa: " Shin za ku kashe Mutum kawai domin yace Allah ne Ubangijina? ". Da sauran Ayoyi masu yawa a wannan fagen.
Musulunci Addinin aiki da Hankali ne da Dogara da Hujjah. Babu inda Allah yayi Umurni ko yayi nuni, a cikin Al-Qur'ani, ko Annabi yayi Ishara a cikin Hadisi da Sirah a kan Mutane su yi Imani da Allah, ko da wani abu da Allah ya fada, rufe da Idanu, ba tare da hujjah mai karfi ba. Hatta Haddodin Shari'ah wadanda hankali ba wani kaso mai yawa yake dashi a cikinsu ba, domin su Imani sukafi bukata fiye da Hankali, duk da haka saida Allah (SWT) ya dora hujjar aikatasu bisa Qa'idojin Hankali ta hanyar Kafa hujja mai inganci.
To itama Harka Islamiyyah a kan haka aka Dorata. Jagoranta Sayyid Allamh a kan haka yake tafiyah. Kai muna iya dakar kirji muce wannan shine Kashin bayan Harkar Musulunci, shine Halsashin da aka dorata a kai. Ta nan ne ta yiwa sauran Fikirori Fintinkau. Idan ka kalleta kallo na Natsuwa da fahimta, to zaga Kafafunta basu doro a kan komai ba, illa saman Sawun Takon Al-kur'ani da Hadisi, a Mihwari da Tafarki.
Wannan ne yasa Muwafaqa da Shari'ah ta zamo Rigar Jagoran Harka, sai kurensa ya Karanta, dai-dansa ya yawaita, harma saboda karancin kuren ya zamo ba'a ganin komai a tattare dashi sai dai-dai. Kai hatta kananan kurarran saboda Girman Ikhlasi sai Allah ya mayar masa dasu dai-dai, cikin Ludufinsa da Dafawarsa ga Bawansa.
Masu ganin ana wuce Gona wajen Girmashi ko an kaishi inda bai kaiba, to su kawo mana wani irinsa wanda tafiyarsa take tako irin takon Al-Qur'ani, take Kwalliya da Kwalliyar Sunnah, take kanshi da Furannin Fikira Sahihiya, irin tashi Tafiyar. Idan babu, to su barmu mu yabi abunmu domin dama ba'a yabon kowa sai Gwarzo.
Wanda Allah ya tsare ya kange daga aikata Kuskure ko Al-fasha da Sabo, na Zahiri da Badini shine Ma'asumi. Mu'utasimi ko wanda ya kankame Allah, ya rungume Dokokin Allah, ya Lizimci Igiyar Allah, domin ta kareshi daga fadawa cikin Kure ko aikata kuskure ko Zunubi. Sai Allah ya masa Muwafaqa da tafiya saman Tozon Gaskiya, ya bashi Hankali Madai-daici. Irinsu ne ake bawa Amanar renon kwakwale da zukatan Al-ummah bayan Fakuwar Ma'asumai.
Daga ka bar Tafarkinsu to sai fagamniya cikin Dajin Dimuwa.
Shamsudeen Hassan