Sayyada Zahara (A's) Kashin Baya ce A Cinkin Tafiyar Addinin Nan!!!



MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041



“Sayyida Zahra (S.A) ƙashin baya ce a cikin tafiyar addinin nan (Musulunci) domin ita da ’ya’yanta su ne amanar addinin nan ya rataya a wuyansu wanda Manzon Allah (S.A.W.W) ya bar ma su kuma ya barwa al’umma. Ita kanta Sayyida din da ’Ya’yanta su babbar amana ce da ya zama wajibi al’umma ta rike, kuma rashin rike wannan gida ya jefa al’umma halin da ta samu kanta ciki. Domin Allah ba azzalumi ba ne, Allah ba ya zalinci, Allah ba ya ƙeta, haka kuma Allah ba ya ta more, haka nan kawai ya wahalar da mutane. Allah ba ya hakanan.


Allah Maɗaukakin Sarki ya na tsara wa mutane shari'a da dokoki in sun bi su samu sa’ada ta duniya da lahira, in sun ki su wahala duniya da lahira kuma shi ne abinda ya sa mu wannan al’umma ɗin dangane da gidan Manzon Allah (S).


In kana magana a kan abinda ya shafi Sayyida Zahra (S.A) da ’ya’yanta; to sunanka kawai dan Shi'a kaman ka ce shi dan Shi'a shi kawai ya san ƙimar gidan Annabi, kamar shi kaɗai ya san wasiyyar Annabi... 


Sauran al'ummar Musulmi kuma su wannan sun riga sun shiga dimuwa harma sun jahilci saƙon Manzon Allah din (S). 


Alhali babu yadda za a yi mutum ya samu tsira tare da saɓa wa Annabi, babu yadda za a yi nan duniya ya samu abinda ya ke so tare da saɓa wa Annabi, ba fa zai yiwu ba to ballantana kuma lahira wanda can wurinsu ne, su ke da ita su zasu raba aljanna...”


’Yan’uwa Musulmi masoya gidan Manzon Allah (S) mu na ma ku barka da shiga watan da Allah ya baiwa ManzonSa kyautar da babu irinta duniya da lahira ita ce Sayyida Zahra (A.S), Hani’al-lana wa lakum”.


- Shaikh Yakub Yahya Katsina


    #SYYK

25Dec2022

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post