Sako Zuwa Ga Iyaye Don Gyaran Tarbiyar Yayansu!!!




Haƙiƙa al'amarin tarbiyyar ƴaƴa musamman ƴaƴa mata, abu ne mai muhimmanci matuƙa, wanda da yawa a wannan lokacin mafi yawan iyaye suka yi sakaci ƙwarai a kan sa.


Za ka samu yarinya ta fara girma ta kai shekara sha biyar 15, amma iyaye ba su damu da ina ta ke zuwa ba, yaushe ta ke dawowa makaranta ; da ƙawayen da ta ke mu'amala da su.


Saboda haka, yana da kyau iyaye sun sanya idanu a kan ƴaƴansu musamman ƴaƴa mata. Akwai wasu shawarwari masu tsada da na tsara zan baiwa iyaye, domin katange ƴaƴansu daga maɓarnata:


1. Sanin waɗanda ƴaƴanku suke mu'amala da su a fili da kuma boƴe?


2. Sanya ido game da suturar da ƴarku/ɗanku suke sanyawa musamman lokacin da za su fita gida.


3. Hanasu kallon wasu tashoshin da ake yaɗa ɓarna da lalata tarbiyya.


4. Dakatar da ita daga fita gun saurayi da sunan soyayya, idan ba aurenta zai yi ba.


5. Sanya ido da bincike a cikin wayoyinsu, da kuma suwa suke mu'amala da su a wayar.


6. Lura da lokacin da suke kwanciya barci da daddare.


7. Sanyasu suyi muraji'ar abin da aka musu a makaranta.


8. Ƙoƙarin zama da su domin jin matsalolinsu, da kuma shawarwari.


9. Ƙulla alaƙa mai ƙarfi tsakaninku da malamansu na boko da Islamiyyah.


10. Bayan kunyi iya bakin ƙoƙarinku sai ku biye da yi musu addu'a, Allah ya shiryar muku da su hanya madaidaiciya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post