Sheikh Zakzaky (H)


Akwai Bukatar Dukkanin Azzalumai da Iyayen Gidansu, Sannan Da Muminai(Ma'abota Addini) Su yi Nazarin Yadda Waki'ar Zaria ta Gudana Sannan.



Mu yi Nazari Sosai Akan Hotunan Malam Zakzaky(H) Da Muka Zayyano su Akwai babban Darasi da Aya Da ya kamata Dukkanin Azzalumai da iyayen Gidansu Su dauka Sannan Muminai ma Akwai Darasi da Aya da Yakin da ya kamata ace Sun dauka a tattare dasu hotunan.



Ban yi Tunanin A Tarihin Nigeria Za a samu Wani Bawan Allah da Aka taba yi wa Mummunan Zalunci Ta Hanyar Yunkurin Kisan kai da Tsarewa da Raunuka ba tare da Kulawa ba, kamar Malam Zakzaky(H) Sannan kuma Allah ya Cigaba da Wanzar da Rayuwarshi har Zuwa Yanzu.


Saninmu ne Waki'ar Zaria Tsararren Shiri ne kuma manufar harin Shine Kashe Malam Zakzaky da Murkushe Harkar iskamiyyan nan gaba daya, sannan Duk Wani Yunkuri da Ake son yi na ganin An yi Nasarar kashe Malam Zakzaky Daga Ta Hanyar Harbinsa na Harsasai a jikinsa, kashe masa 'Ya'yansa Shida, tsare shi da hana shi Neman lafiyar Raunukan da yake fama da su da Amfani da Guba a Abincin da Ake Ciyar da Shi a Tsare, dukkan Wadannan Hanyoyin An bi su ne Don ganin An kashe Malam Zakzaky amma An yi Nasara?


Wani Likitan da yake Kula da lafiyar Malam(H) wata rana yake Cewa gaskiya Zakzaky He's not a Human Being(Wato anasa Tunanin Zakzaky ba Mutum bane) ganin Halin da ya Shiga na Hadari sannan kuma yake Rayuwa.


Hatta Sojojin Da Suka Aiwatar da Kisan kiyashin nan da wadanda Suka Rika Harbin Sheikh Zakzaky da Nufin kashe Shi, sun yi Mamakin Wanzuwarshi a duniya, sannan Su Sun dauke Shi ne ma a lokacin a matsayin Gawa(Matacce) amma daga bisani ya Farfado Hakan yasa Suke Tunanin Malam Zakzaky Na Musamman ne.


To, darasin da ya kamata Dukkanin Azzalumai da iyayen Gidansu Zasu dauka anan Shine, Allah Shi yake kashewa Sannan yake Rayawa kamar yadda Suka ga Zahirin hakan.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post