Yau ne aka Shiga rana ta 3 da taron IVC na dalibai da ake gudanarwa a Abuja, wadda Dandalin Dalibai (AFIM) na harka ya shiryawa Dalibai.
Ana cikin gabatar da darussa da ake gudanarwa a cikin azuzuwa, Sheikh Abba Bature ne ke daukar Darasi akan Fiqhu inda a bangaren yara kanana ya gabatar masu da darasi akan yadda ake Tsarki, Alwalla da Sallah, sannan Sheikh Ishaq Misau ne ke gabatar da darasi akan Akhlaq, sai bada Tarihin Harka Islamiyya na littafin da Malama Zeenah ta rubuta Wanda Mahdi Ali Babba ke karanta masu, sai darasin karshe da Dr. Naziru Shuwaki yayi bayani akan yadda zaa bada taimakon agajin gaggawa.
Ga wasu daga hotunan da muka dauko maku.
19/12/2022.
Tags:
Labaran Duniya