Raddin Dr. Sunusi Abdulkadir Koki ga rahoton 'Dailly Review' mai taken "rikicin rikin gida a Harka"_Nasir Isa Ali

 


              Nasir Isa Ali 


Ranar juma'a 2 ga watan Disamba nan na 2022 ne Wakilin yan'uwa na Kano Dr. Sunusi Abdulkadir Koki ya yi raddi na ilimi ga wani rahoto wanda wata jarida mai suna 'Dailly Review' ta wallafa mai taken 'Rikicin cikinngida a cikin harkar musulunci.


Bayan Dr. ya yi mukaddima game da muhimmancin yi wa Annabi salati, sai kuma bayani kan sadaukarwa da jarumtakar da sayyada Zainab ta yi bayan wakiar Karbala. 

Ya ambato kadan daga cikin rayuwa da shahadar sayyada Fatimatuz Zahra (as) sai kuma magana kan waki'ar Buhari ta Zaria. Sauke Wannan



Ya bayyana cewar wadanda suka aukar da waki'ar ba wai sun sha bane, tabbas akwai ranar daukar fansa na nan tafe.


Dr. Sunusi ya fara raddin nasa ne da karanto wasu bangarorin da suka fi muhimmanci a rahoton sannan ya rika bada amsa ta ilimi kuma gamsasshiya.

Ya bayyana cewar mai rahoton ya yi kokarin raba almajiran jagora zuwa gida biyu waton yan zafi zafi, da kuma yan sanyi sanyi. Dr. Sunusi ya bayyana cewar shi a iya saninsa duk almajiran mallam Zakzaky (H) duk cikarsu abu daya ne, kuma kowannensu ya kan zama mai zafi zafi ne a inda ya dace ayi zafi zafin. Sauke Wannan



Sannan kuma duk cikarsu yan sanyi sanyi ne a inda ya dace ayi sanyi sanyi, don haka mai wannan rahoton bincikensa ya nuna masa karya. 


Yace daman ita rayuwa haka take akwai bangaren yin sanyi sanyi, akwai kuma bangaren yin zafi zafi kuma kowannesu yanayi ne yake haifar dasu.

Ya bayyana cewar maganar wai wasu ne daga almajuran jagora suka yarda addini zai tabbata, amma mafi yawan almajiran mallam Zakzaky (H) wai basu yarda cewar addini zai tabbata ba.

Sai Dr. Sunusi yace ai ba ma su almajiran mallam Zakzaky ba a'a duk wani musulmi yana fatan ya ga addini na iko da rayuwarsa. Suna iya zuwa su kebe da musulmi don su ji raayinsu, kuma duk cikarsu zasu zabi tsarin musulunci ne.

Ya bayyana cewar ai babu musulmin da zai ki yarda rayuwar manzon Allah tayi iko da rayuwarsa.




Ya bayyana cewar bangaren da yafi komai muni a cikin rahoton shine inda suka bayyana cewar wai idan mallam Zakzaky ya koma ga Allah to wai ita ma harkar zata mutu. Domin wai mallam Zakzaky bai da mataimakin da zai gaje shi.

Dr. Sunusu ya bayyana cewar gaskiya ne cewar duk kungiyar da take da tsarin kungiyanci to da zarar wanda ya kafata ya mutu ita ma kungiyar ta kan mutu.

Sai yace amma fa ya kamata kowa ya sani cewar ita fa harka Islamiyya ba kungiya bace, domin da kungiya ce to tun farkon tasowarta zata taso ne da tsarin kungiyanci kamar yadda aka san kowacce kungiya.


Dr. Sunusi ya bayyana cewar harka islamiyya fikira ce ba kungiya ba, don haka babu ranar rushewarta. Ya kara da cewar manzon Allah ne ya zo da musulunci kuma ko da manzo ya koma ga Allah ai musulunci bai rushe ba.

Ya bayyana cewar lokacin da manzo yayi wafati musulmin duniya kakaf basu wuce su dubu 200 ba, amma yau kuma fa? Ana maganar miliyoyin musulmi ne. Ya bayyana cewar hakan ma aka eika fada cewar idan manzo (Muhammadu) ya yi wafati musulunci zai mutu,to gashi har yau ana musulunci kuma sai cigaba yake yi.


Sannan ya bayyana cewar mai yasa da Imam Ali (as) yayi wafati shi'arsa bata mutu ba? Saboda ai fikira ce shiyasa har yau bata mutu ba.

De. Sunusi ya kara bada hujja da cewar a Iran an samu Imamu Khomeini ya jagoranci juyin musulunci har aka kafa gwamnatin musulunci, to me yasa da Imam yayi wafati daular bata rushe ba?


Idan aka yi tambayar cewar menene ke jagorantar Iran a halin yanzu? Sai kace fikirar Imam Khomeini ce ke jagorantar Iran. Shi sayyid Qaid ai wakili ne na fikirar Imam Khomeini (qss)

Haka zalika da aka kashe Imam Hussain sai fikirarsa ta mutu? Gashi har yau muna fadar LABBAIKA YA HUSSAIN.

Don haka ita ma fikirar mallam Zakzaky tazo zama ne daram, kuma har abada ba zata mutu.


A karshe ya saka wa yan'uwa fatan cewar tabbas gwamnatin musulunci zai kafu daram da izinin Allah.

---------

Nasir Abu Muhammad



1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Allah yakara ganardamu gaskiya kuma yabamu. ikon binta bhk amirul muminina(aswl)

    ReplyDelete
Previous Post Next Post